News
Zargin Bai Wa ’Yan Bindiga Makamai: DSP Ya Harbe Kansa A Jihar Neja
Wani babban jami’in ’yan sanda mai mukamin Deputy Superintendent of Police (DSP), Isah Abdullahi, ya mutu a Jihar Neja bayan da ake zarginsa da hannu wajen bai wa ’yan bindiga makamai da harsasai.
Marigayi DSP Isah Abdullahi, wanda aka fi sani da Kunkuri, jami’i ne a rundunar Police Mobile Force (Mopol 12) da ke Minna, kuma shi ne ke kula da ma’adanar makamai a cikin harabar B Division na rundunar ’yan sanda ta jihar.
Cristiano Ronaldo Zai Fito A Mashahurin Fin Ɗin Nan Na Fast & Furious
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne yayin wani binciken shekara-shekara kan makamai da harsasai da tawagar jami’an bincike daga Abuja ke gudanarwa, inda aka gano gibin makamai da dama.
Binciken farko ya nuna cewa bindigogi AK-47 guda 13 da kuma harsasai sama da 2,000 sun ɓace ba tare da bayani ba. An ce an fara binciken ne a ɓangaren bindigogin AK-47, duk da cewa akwai wasu nau’o’in makamai a ma’adanar.
A ci gaba da bincike, jami’an tsaro sun kama wani sufeton ’yan sanda da ke aiki a Gidan Gwamnatin Jihar Niger da ke Minna. Rahotanni sun ce ya bayyana wa masu bincike cewa yana karɓar makamai daga marigayi DSP, wanda ake zargin an kai su hannun ’yan bindiga da ke aiki a ƙauyen Erena da ke Ƙaramar Hukumar Shiroro.
An ce makaman sun kai hannun ’yan bindigar ne ta hanyar ɗan’uwan sufeton, wanda ɗan asalin yankin ne kuma ake zargin yana ba ’yan bindigar bayanan sirri.
Bayan haka ne jami’an Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro (NSA) suka shiga lamarin, inda suka kwashe waɗanda ake zargi zuwa Abuja domin ci gaba da bincike. Daga baya aka dawo da DSP Isah Minna domin gudanar da binciken zahiri kan makaman da ke ma’adanar.
A yayin wannan bincike ne rahotanni suka ce jami’in ya ɗauki bindiga daga cikin ma’adanar, inda ya harbe kansa, ya mutu nan take.
Wasu majiyoyi sun ce ba a ɗaure shi da ankwa ba a lokacin, kasancewar ma’adanar makaman na amfani da tsarin lantarki, kuma shi kaɗai ke da damar shiga cikinta.
Biyo bayan faruwar lamarin, ’yan sandan da suka raka shi wurin binciken an kama su bisa zargin sakaci a bakin aiki, yayin da aka kama wasu jami’ai huɗu da ke aiki tare da marigayin domin yi musu tambayoyi.
Haka kuma, wata tawaga ta musamman daga ofishin NSA ta fara tsaron ma’adanar makaman dare da rana, yayin da ake neman hanyar shawo kan matsalar buɗewa da rufewarta.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Niger, Adamu Elleman, ya ce bincike na ci gaba, kuma sufeton da aka kama yana hannun jami’an tsaro a Abuja.
Ya ce za a gudanar da binciken likitanci (autopsy) domin tantance ainihin musabbabin mutuwar jami’in.
A nasa bangaren, Mai Magana da Yawun ’Yan Sanda na Jihar Niger, DSP Wasiu Abiodun, ya ce an kama DSP Isah tun ranar 15 ga Disamba, bisa zargin safarar harsasai ba bisa ƙa’ida ba, kafin a kai shi ofishinsa domin bincike, inda lamarin ya faru.
Ya ce bincike na ci gaba domin gano duk masu hannu a lamarin.
