Connect with us

Business

Aikin Jarida Ya Koma Intanet: SDJ Ta Sanar da Bude Sabon Zango na Horar da ’Yan Jaridu

Published

on

IMG 20260107 WA0011
Spread the love

A yayin da fasahar zamani ke ci gaba da sauya yadda ake yada labarai, masana na nuna cewa aikin jarida ya koma dandalin intanet, inda ake wallafa labarai, gabatar da shirye-shirye, har ma da samun kuɗi ta kafafen sada zumunta.

A cikin wannan yanayi ne School of Digital Journalism (SDJ) ta sanar da shirin bude daukar sabbin ɗalibai, da nufin horas da masu sha’awar aikin jarida dabarun zamani da suka shafi kafafen yanar gizo.

Trump Ya Ce Daga Yanzu Shi Zai Rika Juya Kudaden Man Venezuela

A cewar bayanan makarantar, SDJ na koyar da rubuta labarai da rahotanni, kirkirar kafafen yada labarai a shafukan Facebook, TikTok da YouTube, da kuma gabatar da shirye-shirye irin su tattaunawa (talk show), hira (interview) da podcast.

Haka kuma, makarantar na bai wa ɗalibai horo kan hanyoyin samar da kuɗaɗe ta aikin jarida na online, abin da ke kara samun sabbin damammaki a fagen yada labarai na zamani.

Advertisement

An ce daukar ɗaliban zai fara ne a ranar 10 ga watan Janairu, 2026, yayin da ofishin makarantar ke kan titin Zariya Road, kusa da BF Suma.

Masu sha’awar samun karin bayani za su iya tuntubar makarantar ta lambar waya 08033132660.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *