Connect with us

News

Trump Ya Ce Daga Yanzu Shi Zai Rika Juya Kudaden Man Venezuela

Published

on

Donald trump
Spread the love

Shugaban na Amurka Donald Trump ya ce za a sayar da man sannan kudin zai amfani ‘yan Venezuela da Amurkawa.

Trump ya ce ya bayar da umurni nan take a aiwatar da wannan matakin.

Haka zalika Trump, ya fada cewa gwamnatin rikon kwarya ta Venezuela za ta mika gangan mai tsakanin miliyan 30 zuwa miliyan 50 na da ke karkashin takunkumi ga Amurka, a wani mataki da ya ce zai amfani kasashen biyu.

Advertisement

Fadan ’Yan Daba A Kano: Mutum Daya Ya Rasa Rai, ’Yan Sanda Sun Kama Mutum 9

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce za a sayar da man fetur din a farashi mai kyau, kuma kudaden da aka samu za su kasance karkashin ikonsa a matsayinsa na shugaban kasa domin tabbatar da cewa an yi amfani da su “ga al’ummar Venezuela da na Amurka.

Trump ya ce ya umurci Sakataren Makamashi, Chris Wright, da ya aiwatar da wannan shiri nan take domin a cimma moriyarsa.

Za a dauki man ne ta jiragen ruwa, sannan a kai shi zuwa tashoshin sauke kaya a Amurka kai tsaye, in ji Trump.

Advertisement

A ranar Asabar, Amurka ta kai hare-hare kan wasu wurare a Venezuela, inda ta kama shugaban kasar, Nicolás Maduro, bisa zarginsa da safarar miyagun kwayoyi, tare da fitar da shi daga kasar zuwa Amurka.

Bayan wannan farmaki, Trump ya ce Amurka za ta rika gudanar da Venezuela na dan lokaci sannan man kasar zai koma karkashin kulawar Amurka.

Advertisement
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *