Connect with us

News

Kotu Ta Bayar Da Belin Abubakar Malami Da Iyalinsa Kan Naira Miliyan 500

Published

on

Malami son and wife

Kotun Tarayya da ke Abuja ƙarkashin jagorancin alƙali Emeka Nwite ta amince da bayar da belin tsohon ministan shari’a Abubakar Malami da iyalinsa kan kuɗi naira miliyan 500 da kuma mutum biyu da za su tsaya musu.

Advertisements
Advertisements

A cewar alƙalin, mutanen da za su tsaya musu sai sun kasance suna da filaye a yankunan Asokoro da Maitama ko Gwarinpa, sannan kuma sai sun miƙa dukkan takardun tafiyarsu ga kotu.

Advertisements

Aikin Jarida Ya Koma Intanet: SDJ Ta Sanar da Bude Sabon Zango na Horar da ’Yan Jaridu

Kwanakin baya ne dai hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC ta gabatar da tuhume-tuhume 16 a kan Malami da iyalinsa masu alaƙala da halasta kuɗaɗen haram da kuma mallakar kadarori da darajarsu ta haura naira biliyan 8.7 wanda ya kai ga tsaresu a gidan yarin Kuje da ke Abuja.

Advertisements
Advertisements
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending