Sports
Senegal Ta Lashe Gasar AFCON Bayan Doke Mai Masaukin Baƙi
Senegal ta zama zakarar Gasar Nahiyar Afirka (AFCON) ta 2025, bayan doke mai masaukin baƙi, Maroko da ci ɗaya mai ban haushi a wasan ƙarshe na gasar.
Ɗan wasan tsakiyar Senegal, Pape Gueye ne ya jefa ƙwallo ɗaya tilo a raga a minti na 94, bayan shafe minti 90 ba tare da zura ƙwallo a raga ba.
Ƙwallon tasa ta bai wa ƙasarsa damar sake lashe gasar a karo na biyu a tarihinta.
Wasan dai ya ɗauki zafi lokacin da alƙalin wasa ya bai wa Maroko bugun fenariti a minti na 96, lokacin dana daf da tashi daga wasan.
Wasan hukunci ya janyo taƙaddama lamarin da ya sanya kocin Senegal bai wa ’yan wasansa umarnin ficewa daga filin.
Sai dai ɗan wasan gaban Maroko Brahim Diaz ya ɓarar da fenaritin, inda mai tsaron ragar Senegal Edourd Mendy ya damƙe ƙwallon.
’Yan wasan ƙasar Senegal sun koka kan yadda alƙalin wasan ya jagoranci wasan, inda suka yi zargin ya yi wa masu masaukin baƙi alfarma.
Wannan ba shi ne karon farko da aka yi ƙorafi kan cewa ana yi wa Maroko alfarma tun bayan fara gasar ba.
A wasan da Maroko ta fitar da ƙasar Kamaru, an yi ƙorafin cewa an yi wa mai masaukin baƙi alfarma.
Hakazalika magoya bayan tawagar Super Eagles na Najeriya sun koka a wasan kusa dana ƙarshe da suka buga da Maroko.
