News
BSAF-HCAN Ta Jinjinawa jami’an ’Yan Sanda Bisa Gagarumar Nasarar Kama Wadanda Ake Zargi da Kisan Mutane 7 A Dorayi
Kungiyar BSAF Health and Cancer Advocacy Network (BSAF-HCAN) ta yabawa Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano bisa gaggawar daukar mataki tare da nasarar kama wadanda ake zargi da aikata mummunan kisan ’yan gida daya su bakwai (7) a unguwar Chiranci Dorayi, dake Karamar Hukumar Gwale, Jihar Kano.
Ta cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Nura Auwalu Uba, shugabar kungiyar Hajiya A’isha Usman Danjika, ta bayyana cewa wannan aikin da ƙwarewa da Rundunar ’Yan Sandan tayi hujja ce ta jajircewarsu wajen kare rayukan al’umma da tabbatar da adalci. Danjika ta ce wannan mataki ya taimaka wajen kwantar da hankulan al’umma a yankin dama jihar Kano baki daya.
Fiye Da Musulmai Miliyan Uku Sun Halarci Mauludin Sheikh Ibrahim Niasse Karo Na 40 A Katsina
BSAF-HCAN na mika ta’aziyyarta ga iyalan waɗanda suka rasa rayukan nasu da kuma al’ummar Dorayi,Gwamnatin, dama Al’ummar Kano baki ɗaya bisa wannan mummunan ibtila’i. Kungiyar ta jaddada cewa irin wannan lamari yana da matukar tasiri ga lafiyar kwakwalwa da walwalar al’umma, musamman ga waɗanda abin ya shafa kai tsaye.
Yayin da take yaba wa Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano bisa wannan namijin ƙoƙari, Shugabar kungiyar ta BSAF Hajiya A’isha Usman Danjika na kira da a gudanar da cikakken bincike tare da tabbatar da ganin an hukunta duk wanda aka samu da laifi bisa doka. Haka kuma, kungiyar na kira ga ci gaba da haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro, shugabannin al’umma da kungiyoyin farar hula domin hana faruwar irin wannan lamari a nan gaba, tare da magance matsalolin zamantakewa da na lafiyar kwakwalwa.
BSAF-HCAN ta sake jaddada kudirinta na ci gaba da fafutukar kare rayuka, inganta lafiyar jama’a, samar da zaman lafiya da walwalar al’umma a Jihar Kano da ma kasa baki ɗaya.
-
News4 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News2 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News4 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
