News
Fiye Da Musulmai Miliyan Uku Sun Halarci Mauludin Sheikh Ibrahim Niasse Karo Na 40 A Katsina
Fiye da Musulmai miliyan uku daga sassa daban-daban na Najeriya da wasu ƙasashen Afirka ne suka hallara a Jihar Katsina domin halartar bikin Mauludin marigayi jagoran darikar Tijjaniyya, Sheikh Ibrahim Niasse.
An gudanar da taron na tsawon mako guda a filin wasa na Dukko Radda da ke birnin Katsina, karkashin jagorancin ƙungiyar Majma’u Ahbab Niasse.
Wasu Bata Gari Sun Hallaka Mutune 7 Ciki Har Da Jaririya A Kano
Masu shirya taron sun bayyana cewa bikin na bana ya kasance na musamman, kasancewarsa karo na 40 da ake gudanar da wannan gagarumin taro na addini.
Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban ƙungiyar Majma’u Ahbab Niasse, Sheikh Ahmad Tijjani Sani Auwal, ya ce an shirya Mauludin ne domin tunawa da rayuwa da koyarwar Sheikh Ibrahim Niasse, tare da yin addu’o’i na neman zaman lafiya, haɗin kai da cigaban tattalin arziki a Jihar Katsina da Najeriya baki ɗaya.
Sheikh Auwal ya bayyana cewa wannan ne karo na uku da Katsina ke karɓar bakuncin taron, bayan na shekarun 2002 da 2016. Ya kuma ce jihohin Zamfara, Sakkwato da Kebbi sun taɓa ɗaukar nauyin irin wannan taro a baya.
Ya yaba wa gwamnatin Katsina bisa samar da yanayi na zaman lafiya, yana mai cewa hakan ya taimaka wajen gudanar da taron cikin kwanciyar hankali.
A nasa jawabin, Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi na II, ya yi kira ga mabiya darikar Tijjaniyya da sauran Musulmi da su zauna cikin haɗin kai da fahimtar juna.
Ya bayyana Sheikh Ibrahim Niasse a matsayin malami mai matuƙar tasiri, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen yaɗa addinin Musulunci a sassan nahiyar Afirka.
Shi ma Gwamnan Jihar Katsina, Dr. Dikko Umaru Radda, ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa ayyukan addini da ke inganta zaman lafiya, haɗin kai da zaman tare.
Taron ya samu halartar manyan baki daga Najeriya da ƙasashen Yammacin Afirka, ciki har da wakilan Kungiyar Haɗin Kan Ƙasashen Musulmi (OIC), da kuma wakilan Khalifan Niasse daga ƙasar Senegal.
An kammala Mauludin ne a ranar Asabar, bayan kwanaki bakwai na karatun Alƙur’ani, addu’o’i, wa’azuzzuka da tarukan ilmantarwa, waɗanda suka mayar da hankali kan rayuwa, koyarwa da tasirin Sheikh Ibrahim Niasse.
