Connect with us

News

‎Wasu Bata Gari Sun Hallaka Mutune 7 Ciki Har Da Jaririya  A Kano

Published

on

Hukumomi a Najeriya sun tsaurara matakan tsaro da kuma sa ido sosai a birnin Kano,

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta ce ta fara gudanar da bincike kan wani mummunan kisan gilla da aka yi wa wata mata da ’ya’yanta shida a unguwar Dorayi Chiranchi da ke cikin birnin Kano.

‎Ta ce ta samu kiran gaggawa da misalin karfe 12:10 na rana a ranar 17 ga Janairu, 2025, inda aka sanar da su cewa wasu da ba a san ko su waye ba sun kai hari gidan Haruna Bashir.

Advertisement

An Kama Matashi Bisa Yunƙurin Shigar Da Tabar Wiwi Gidan Gyaran Hali A  Kano 

‎Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya aikowa Jaridar INDA RANKA ranar Asabar

‎Sanarwar ta kuma bayyana cewa matar, Fatima Abubakar mai shekaru 35 da ’ya’yanta shida, sun samu munanan raunuka bayan da maharan suka shiga gidansu tare da amfani da muggan makamai akan su.

Advertisement

‎Bayan samun rahoton, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya umarci wata tawaga ta musamman karkashin jagorancin Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda mai kula da ayyuka, DCP Lawal Isah Mani, da su gaggauta zuwa wajen da abin ya faru.

‎Sanarwar ta ce tuni an kwashe gawarwakin wadanda abin ya shafa zuwa Asibitin Murtala Mohammed da ke Kano, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsu.

Advertisement

‎Hakazalika, Kwamishinan ’Yan Sandan ya ba wa tawagar binciken manyan laifuka ta CID, karkashin jagorancin ACP Wada Jarma, umarnin gudanar da cikakken bincike domin gano wadanda suka aikata wannan aika-aika tare da gurfanar da su a gaban shari’a.

‎Rundunar ’Yan Sandan ta kuma mika sakon ta’aziyya ga iyalan mamatan, da al’ummar Dorayi Chiranchi, da kuma daukacin al’ummar Jihar Kano.

Advertisement

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending