Connect with us

News

Dakarun Sojin Sama Sun Kashe Fiye Da ‘Yan Bindiga 40 A Borno

Published

on

FB IMG 1766746714006

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta bayyana cewa ta kashe fiye da ‘yan bindiga 40 a hare-haren sama da ta kai a wasu sassan Jihar Borno, a yankin Arewa maso Gabashin ƙasar.

Cikin wata sanarwa da Daraktan Hulɗa da Jama’a na rundunar, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya fitar a ranar Lahadi, ya ce hare-haren sun taimaka wajen tarwatsa wani shiri da ‘yan bindigar ke yi na kai hare-hare, tare da ba sojojin ƙasa damar ci gaba da aikinsu a yankunan da lamarin ya shafa.

Senegal Ta Lashe Gasar AFCON Bayan Doke Mai Masaukin Baƙi

A cewar Ejodame, an kai hare-haren ne a ranakun 15 da 16 ga watan Janairu, bayan samun bayanan sirri da kuma haɗin gwiwa da dakarun sojin ƙasa da ke aiki a yankin.

Sanarwar ta ce jiragen yaƙin sojin saman sun kai ɗaukin gaggawa ne bayan samun rahoton cewa sojojin ƙasa na fafatawa da ‘yan bindigar a wani yanki, lamarin da ya sa aka tura jirage domin tallafa musu.

Ejodame ya ƙara da cewa bayan harin farko, jami’an rundunar sun lura da cewa wasu daga cikin ‘yan bindigar sun sake taruwa a ƙarƙashin wata bishiya, lamarin da ya sa aka sake kai musu hari.

Haka kuma, rundunar ta ce kwana guda kafin hakan, an kai wani hari a yankin Tumbuns, inda aka hango kwale-kwale guda 10 dauke da mayaƙa fiye da 40, wadanda ake zargin suna shirin kai hari garin Baga da kuma madatsar kamun kifi.

Advertisement

Rundunar Sojin Sama ta ce za ta ci gaba da kai irin wadannan hare-hare a matsayin wani bangare na kokarinta na daƙile hare-haren kungiyoyin da ke tayar da hankali a yankin.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending