News
Dakarun Soji Sun Kashe ’Yan Ta’adda 438 Na Boko Haram da ISWAP Cikin Watanni Bakwai
Dakarun Sojin Najeriya sun ce sun kashe aƙalla ’yan ta’adda 438 daga ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP a cikin tsawon watanni bakwai da suka gabata, yayin da ake ci gaba da kai hare-hare kan sansanonin ’yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas.
Kwamandan rundunar Operation Hadin Kai, Manjo Janar Abdulsalam Abubakar ne, ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a Maiduguri, yayin taron cin abincin Kirsimeti na shekarar 2025 da aka shirya wa sojojin da ke bakin aiki a yankin.
A cewarsa, a cikin wannan lokaci sojojin sun kuma kwato makamai 254 iri-iri, tare da na’urorin sadarwa na Starlink kusan 300, waɗanda ’yan ta’addan ke amfani da su wajen sadarwa da tattara bayanan sirri.
Manjo Janar Abubakar ya ƙara da cewa rundunar ta ceto fararen hula 366, ciki har da mata da ƙananan yara, daga maboyar ’yan ta’adda da ke sassan yankin Arewa maso Gabas.
Ya ce mika wuya da ’yan ta’adda 881 daga Boko Haram da ISWAP, tare da iyalansu, suka yi a wannan lokaci na nuna irin raunin da ƙungiyoyin ke fuskanta sakamakon matsin lambar soji.
Kwamandan rundunar ya bayyana nasarorin da aka samu a matsayin sakamakon jajircewa da ƙwarewar sojoji, duk da ƙalubalen da ke tattare da ayyukan tsaro a yankin.
Ya kuma ce bikin Kirsimeti ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da ayyukan soji na lokacin rani, lokacin da rundunar ke ƙara matsa lamba kan sansanonin ’yan ta’adda.
Manjo Janar Abubakar ya tabbatar wa Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, cewa sojojin za su ci gaba da kai farmaki kan ’yan ta’addan har sai an samu zaman lafiya mai ɗorewa a yankin Arewa maso Gabas.
Ya danganta nasarorin da aka samu da ingantaccen tallafin kayan aiki, jin daɗin sojoji, ƙarin makamai da haɗin bayanan sirri, tare da yabawa da haɗin gwiwar hukumomin tsaro daban-daban.
