Politics
Sauya Sheka Ba Cin Amana Bane, Abba Yana Da ‘Yancin Zabi —Shekarau
Tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya ce bai dace a zargi Gwamna Abba Kabir Yusuf da cin amana ba kan rade-radin sauya sheƙa daga NNPP. Ya jaddada cewa sauya sheƙa shawara ce ta mutum, bisa yanayi da shawarwari da magoya baya.
Shekarau ya soki kalaman Rabi’u Musa Kwankwaso da ke cewa Abba ya ajiye kujerarsa idan ya bar NNPP, yana tuna cewa Kwankwaso kansa ya taɓa sauya sheƙa da kujerar gwamna a baya. Ya ƙara da cewa irin wannan al’ada ta riga ta samu misali.
Sauya Sheka Ba Cin Amana Bane, Abba Yana Da ‘Yancin Zabi —Shekarau
Ya kuma bayyana cewa rikice-rikicen rabon Tikiti a NNPP ne suka sa shi yaqi amincewa da tayin kwankwaso a baya wanda hakan yasa ya fice daga jam’iyyar, ya kuma kara da cewa bai dace a kalli duk sauya sheƙa a matsayin cin amana ba, muddin an yi ta da hujjoji kuma magoya baya sun amince.
