Connect with us

News

NAWOJ da KOMC Sun Yaba da Bitar Yini Daya da Aka Basu Kan Fasahar Al da Dabarun Aiki

Published

on

1767695810134

Ƙungiyar Mata ’Yan Jarida ta Najeriya (NAWOJ), reshen Jihar Kano, tare da Kungiyar Mawallafa Jaridun Yanar Gizo na Kungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ), reshen jihar Kano wato Kano Online Media Chapel, sun yaba da taron bitar horaswa na yini guda da aka shirya domin ƙarfafa ƙwarewar ’yan jarida kan fasahar Artificial Intelligence (AI) da kirkirar abubuwan wallafa labarai.

‎An shirya taron bitar ne a Kano domin bikin cikar Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo shekaru 38 da haihuwa, inda aka gudanar da shi a Dakin Karatu na Murtala Muhammad.

Jirgin Yakin Amurka Sunfurin US Air Force C 130 Ya Sauka A Abuja

‎Taron, mai taken ““The Role of Artificial Intelligence and Content Creation: Impact in the Year 2026”, ya samu gabatarwa daga Musa Abdullahi Sufi, tare da halartar ’yan jarida, masu kirkirar abun ciki da mambobin ƙungiyoyin biyu.

‎Shugabar NAWOJ reshen Jihar Kano, Sayyida Bahijja Malam Kabara, da Shugaban Kungiyar ’Yan Jaridar Yanar Gizo ta Kano, Kwamared Abubakar Abdulkadir Dangambo, sun ce horon ya zo a daidai lokacin da fasahar AI ke kara tasiri a aikin jarida da hanyoyin yada labarai.

‎A cewarsu, taron ya taimaka wajen kara fahimtar yadda za a yi amfani da AI cikin tsari da ɗa’a, tare da inganta kirkira da sahihancin labarai a wannan zamani na sauyin fasaha.

‎Shugabannin ƙungiyoyin sun bukaci mahalarta taron da su yi amfani da ilimin da suka samu domin inganta kwarewa da bin ka’idojin aikin jarida, musamman yayin da ake tunkarar sabbin kalubale a fagen yada labarai nan gaba.

Advertisement

‎Ƙungiyar NAWOJ reshen Jihar Kano da Kungiyar ’Yan Jaridar Yanar Gizo ta Kano sun kuma yaba wa Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo bisa amfani da bikin ranar haihuwarsa wajen tallafa wa ilimi da ci gaban aikin jarida.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending