News
Boko Haram Ta Sake Kai Hari Kan Sansanoni Biyu Na Soji A Borno
Wasu mayaƙan Boko Haram sun kai hare-hare kan sansanonin sojojin Najeriya guda biyu da ke Jihar Borno, inda suka kashe wasu sojoji, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.
Mayaƙan sun kai hare-haren ne a sansanonin soji da ke yankunan Kale-Balge da Gajiram da ke jihar. Har zuwa yanzu, ba a fitar da cikakken bayani ba kan adadin sojojin da suka rasa rayukansu ko irin barnar da aka yi.
Majalisar Kano Ta Amince Da Kafa Hukumar Hukunta Masu Karya Dokar Hanya
FRI HAUSA ta ruwaito cewa an ji karar harbe-harbe na tsawon lokaci, lamarin da ya jefa jama’a cikin fargaba, inda da dama suka gudu daga gidajensu.
Wannan hari na zuwa ne kasa da awanni 24 bayan wani makamancin sa da aka kai wa sojoji a garin Marte, wanda ke a yankin Arewa maso Gabashin jihar.
Hukumomin tsaro dai ba su ce komai ba tukuna kan harin.
