News
Majalisar Kano Ta Amince Da Kafa Hukumar Hukunta Masu Karya Dokar Hanya
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da kafa sabuwar hukuma da za ta rika hukunta masu karya dokokin hanya a fadin jihar.
Majalisar ta amince da dokar kafa hukumar ne bayan ta kammala karatu na uku na kudurin dokar a zaman ta na ranar Talata.
Mun Rufe Dakunan Kwanan Dalibai Saboda kin bin ƙa’idojinmu —MAAUN
Shugaban masu rinjaye na majalisar, Hon. Lawan Hussaini Dala, ya ce sabuwar hukumar za ta rika kama, ci tarar da gurfanar da duk wanda ya karya dokokin ababen hawa a Kano.
Ya ce, “Wannan hukuma za ta taimaka wajen dakile rashin bin doka da kuma tabbatar da tsari a harkokin zirga-zirga a jihar.”
Majalisar ta ce da zarar Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rattaba hannu a kan dokar, za a fara aiki da ita nan take.
Ana sa ran hukumar za ta taimaka wajen rage cunkoso da hadurra a manyan tituna da kuma kara wa gwamnati kudin shiga.
-
News2 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
