News
Majalisar Dattawa Ta Amince Da Kudurin Gyaran Dokar Zaɓe Bayan Tattaunawa Mai Tsawo
Majalisar Dattawan Najeriya, a ranar Laraba, ta amince da kudurin gyaran Dokar Zaɓe bayan shafe kusan awanni biyar ana tattauna shi sashi-sashi a zauren majalisar.
Kudurin, wanda shi ne kaɗai batun da ke gaban majalisar a zaman na ranar, ya zo ne bayan kammala zaman bankwana da aka yi domin girmama marigayi Sanata Okey Ezea. Daga bisani, majalisar ta koma zama kwamitin majalisar baki ɗaya domin yin cikakken nazari a kan kudurin.
A yayin zaman, ‘yan majalisar sun amince da dukkan sassa 155 da kudurin ya ƙunsa, inda aka yi wa wasu tanade-tanade gyare-gyare, yayin da aka bar mafi yawansu kamar yadda aka gabatar da su tun farko.
Daya daga cikin manyan gyare-gyaren da aka amince da shi shi ne rage wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) wa’adin sanar da jadawalin zaɓe daga kwanaki 360 zuwa kwanaki 180 kafin ranar kaɗa ƙuri’a.
Sai dai majalisar ta ƙi amincewa da tanadin aika sakamakon zaɓe kai tsaye (real-time), inda ta bar tanadin tura sakamakon zaɓe ta hanyar lantarki kamar yadda Dokar Zaɓe ta shekarar 2002 ta tanada.
Masu sharhi na siyasa na ganin cewa sabbin tanade-tanaden na iya janyo muhawara, musamman daga ƙungiyoyin farar hula da jam’iyyun adawa, waɗanda ke kira da a faɗaɗa amfani da fasahar zamani domin ƙarfafa gaskiya da amincewa da sakamakon zaɓe a Najeriya.
