Connect with us

News

Wani Mutum Ya Mutu Yayin Ƙoƙarin Ceto Akuya A Cikin Rijiya

Published

on

One of the officials of the state Fire Service trying to recover the corpse from the well in Saki 708x430 (1)
Spread the love

Wani mutum mai kimanin shekaru 45 ya rasu a garin Saki da ke Jihar Oyo, bayan da ya shiga wata rijiya mai zurfi da ke da ruwa ciki domin ceto wata akuya da ta faɗa ciki.

Hukumar kashe gobara ta Jihar Oyo ta ce ta samu rahoton lamarin ne da misalin karfe 10:23 na daren Litinin, bayan wani kiran gaggawa da wani mutum mai suna Yusuf Ismail ya yi.

Kotu Ta Yanke Wa Shugaban Kamfani Hukuncin Daurin Shekaru 48 Kan Damfarar Fiye Da Mutum 5,000 ‎

A cikin wata sanarwa da ya fitar a birnin Ibadan, shugaban hukumar, Moroof Akinwande, ya ce jami’an hukumar sun isa wajen da lamarin ya faru cikin gaggawa, inda suka tarar da mutumin ya makale a cikin rijiyar.

Advertisement

Akinwande ya ce jami’an kashe gobarar, karkashin jagorancin PFS II Kolade Taiwo, sun yi ƙoƙarin ceto mutumin ta amfani da kayan aiki na musamman, sai dai bayan fitar da shi daga rijiyar, an tabbatar da cewa ya riga ya rasu.

Rahoton ya nuna cewa mamacin ya shiga rijiyar ne da nufin ceto akuya da ta faɗa ciki, amma ya kasa fita daga rijiyar sakamakon zurfinta.

Shugaban hukumar kashe gobarar ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin, tare da yin kira ga jama’a da su guji shiga rijiyoyi ko wuraren da ke da haɗari,

 

Advertisement

(NAN)

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *