Sports
Ousmane Dembele Ya Lashe Kyautar FIFA Mafi Girma
Dan wasan Faransa na kungiyar Paris Saint-Germain Ousmane Dembele ya lashe kyautar FIFA mafi girma ta nuna bajinta a rukunin maza a kasar Qatar.
Tsohon dan wasan gaba na Borussia Dortmund da Barcelona, Dembele, wanda ke cikin tawagar Faransa da ta lashe Kofin Duniya a 2018, ya zura kwallaye 35 a dukkanin gasanni, tare da taimaka wa PSG lashe gasar kalubale da lig na Faransa da kuma kofin zakarun Turai.
Akalla Mutane 54 Ne Suka Mutu Sakamakon Cizon Maciji A Gombe —Ma’aikatar Lafiya
Kazalika, Aitana Bonmati ta kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta lashe kyautar. Sannan kocin PSG ‘dan kasar Sipaniya Luis Enrique ya samu kyautar mai horaswa da ya fi kowanne a cikin tawagar maza, a gaban Hansi Flick na Barcelona da kuma kocin Liverpool da ya lashe gasar Premier Arne Slot.
