Connect with us

News

Akalla Mutane 54 Ne Suka Mutu Sakamakon Cizon Maciji A Gombe  —Ma’aikatar Lafiya

Published

on

Snake

Akalla mutane 54 ne suka rasa rayukansu sakamakon cizon maciji a Jihar Gombe a shekarar 2025, kamar yadda Ma’aikatar Lafiya ta jihar ta bayyana.

Likitan kula da yaɗuwar cututtuka (State Epidemiologist), Dr. Nuhu Bile, ya bayyana hakan ne yayin taron Kwamitin Kula da Matsalolin Gaggawa na Lafiyar Jama’a (S-PHEMC) da aka gudanar a Gombe ranar Talata.

Advertisement

Jami’an Hisbah Sun Kama Wata Mota Da Ta Yi Jigilar Giya Daga Legas Zuwa Kano

Dr. Bile ya ce a bana, mutane 1,591 ne suka kai rahoton cizon maciji a Asibitin Kula da Cizon Maciji na Kaltungo, inda 54 daga cikinsu suka mutu.

Ya bayyana cewa adadin cizon maciji a bana shi ne mafi ƙanƙanta cikin shekaru huɗu, inda aka samu 2,794 a 2022, 2,594 a 2023, da 2,189 a 2024.

Advertisement

Sai dai ya jaddada cewa raguwar ba ta nuna ragin matsalar ba, illa dai rashin wadataccen maganin rigakafin cizon maciji (anti-snake venom) kyauta, lamarin da ya tilasta mutane da dama komawa hanyoyin magani na daban.

Ya ƙara da cewa galibin waɗanda suka samu cizon maciji na zuwa asibiti ne  kawai idan lamarin ya yi tsanani.

Advertisement

Game da sauran cututtuka, Dr. Bile ya ce an samu mutane 176 da suka kamu cutar kwalara a 2025, inda biyar suka mutu, yayin da aka samu Mutum 14 na zazzaɓin Lassa, inda takwas suka rasa rayukansu.

 

Advertisement

SOLACEBASE

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending