News
Jirgin Sama Ya Yi Hatsari A Imo
Mutane hudu sun tsira daga mutuwa bayan wani ƙaramin jirgin sama ya yi hatsari a Filin Jirgin Sama na Sam Mbakwe da ke Owerri, a Jihar Imo, a daren Talata.
Jirgin ƙirar Cessna 172, mallakin kamfanin Skypower Express, ya fuskanci matsala ne da misalin karfe 6:58 na yamma, yayin da yake ƙoƙarin sauka a Runway 17, in ji Hukumar Binciken Tsaron Sufuri ta Najeriya (NSIB).
A cewar Daraktar Hulɗa da Jama’a ta NSIB, Bimbo Oladeji, jirgin na kan hanyarsa ne daga Kaduna zuwa Port Harcourt, kafin matukan jirgin su ayyana gaggawa tare da karkata zuwa Owerri.
Bayan samun kiran neman taimako, jami’an tsaro na filin jirgin sama da ma’aikatan agajin gaggawa sun isa wurin cikin hanzari, inda suka ceto duk mutanen da ke cikin jirgin.
Rahoton ya ce duk mutanen da ke cikin jirgin ma’aikatan jirgin ne. Biyu daga cikinsu na cikin koshin lafiya, yayin da sauran biyun da suka suma a farko aka kai su asibiti domin duba lafiyarsu.
NSIB ta tabbatar da cewa ta fara bincike kan musabbabin lamarin, tare da bayyana cewa za ta sanar da jama’a duk wani sabon bayani da aka samu.
