Politics
’Yan Majalisar Dokokin Kano Sun Goyi Bayan Shirin Gwamna Abba Kabir Yusuf Na Ficewa Daga NNPP Zuwa APC
’Yan Majalisar Dokokin Jihar Kano sun bayyana goyon bayansu ga shirin da ake cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ke yi na ficewa daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar APC, suna masu danganta hakan da rikice-rikicen shugabanci da shari’o’in kotu da ke addabar jam’iyyar.
Shugaban masu rinjaye na Majalisar, Lawan Hussaini, ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai, inda ya ce ci gaba da kasancewa a Cikin NNPP na iya jefa gwamna da sauran zababbun shugabanni cikin shari’a.
Kotu Ta Yanke Wa Wani Mutum Hukuncin Kisa Bisa Kashe Jariri A Kano
A cewarsa, jam’iyyar na fama da bangaranci da kuma rikice-rikicen cikin gida da ke sanya ayar tambaya kan sahihancin tsarinta da tsarin tsayar da ’yan takara a zabuka masu zuwa.
“Akwai hukuncin kotu da ya amince da wani bangare na jam’iyyar. Ba za mu iya ci gaba da zama a NNPP ba mu kuma jefa kanmu cikin irin abin da ya faru a Zamfara,” in ji Hussaini.
Ya ce Majalisar na marawa kiraye-kirayen da ake yi wa Gwamna Yusuf da jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, baya domin su sauya sheka zuwa jam’iyyar da ta fi kwanciyar hankali ta fuskar siyasa.
Hussaini ya kuma yi gargadin cewa idan rikice-rikicen jam’iyyar suka ci gaba, kotu na iya yanke hukuncin cewa ’yan takarar NNPP ba su da ingancin tsayawa Takara, ko da sun lashe zabe.
KWANKWASO YA GARGADI MASU SHIRIN BARIN KWANKWASIYYA
A wani bangare, jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya gargadi mambobin da suka sauya sheka ko ke shirin yin hakan, yana mai cewa sauyin jam’iyya ba ya faruwa ba tare da dalili ba.
Ya ce da dama daga cikin masu sauya sheka a baya sun yi hakan ne saboda moriyar kashin kai, amma daga bisani suka yi nadama.
“Wasu suna bin inda suke ganin nasara take, ba tare da la’akari da abin da zai biyo baya ba,” in ji Kwankwaso.
Ya kara da cewa cin amana na barin tabo a rayuwar mutum, ba a siyasa kadai ba, har ma a zamantakewa.
NNPP TA YI WATSI DA UMARNIN KOTU KAN SHUGABANNINTA A KANO
A wani ci gaba kuma, bangaren NNPP na kasa ya yi watsi da umarnin wata kotu a Kano da ta soke rushe shugabannin jam’iyyar a matakin jiha, kananan hukumomi da mazabu.
Sakataren yada labaran jam’iyyar, Ladipo Johnson, ya ce ba a mika musu wata takardar kotu ba, don haka suna kallon labarin a matsayin jita-jita.
Jam’iyyar ta ce ko da hukuncin ya wanzu, ba shi da inganci, domin kotuna ba sa tsoma baki a cikin harkokin cikin gida na jam’iyyun siyasa.
