News
Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, Ya Mayar Da Martani Akan Gayyatar Da Ganduje Ya Yi Masa Na Neman Shiga Jam’iyyar APC
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf, ya mayar da martani akan gayyatar da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Ganduje ya yi masa na neman shiga jam’iyyar APC.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne Ganduje ya gayyaci gwamnan jihar, da mukarrabansa, da sauran ‘ya’yan jam’iyyarsa ta NNPP, da su koma jam’iyyar APC, domin bunkasa jam’iyyar a jihar Kano.
Yadda faduwar darajar Naira ke yin illa ga kasuwanci a Najeriya a Najeriya
Shugaban jam’iyyar APC na kasa ya ce shawarar gayyatar gwamna Yusuf da sauran ‘ya’yan jam’iyyar NNPP a jihar na daga cikin kudurorin da aka fadada taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC na jihar Kano da aka gudanar a Kano.
“Mu masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a jihar Kano mun yanke shawarar gayyatar gwamnan jihar Kano da jami’an sa da jam’iyyarsa ta NNPP zuwa babbar jam’iyyar mu ta APC.
“Kofofin jam’iyyarmu a bude suke domin tarbar ku da sauran ‘ya’yan jam’iyyar NNPP zuwa APC kuma muna samar muku da wani yanayi da zai ba ku damar shiga jam’iyyar mu,” inji shi.
Gwamna Ganduje ya ce da yawa daga cikin Sanatoci da ‘yan Majalisar Wakilai sun shigo jam’iyyar, kuma nan ba da jimawa ba wasu Gwamnonin ma za su shiga jam’iyyar, inda ya ce, “Idan za mu iya yin hakan a matakin kasa, me ya sa ba za mu iya yin ta a matakin jiha ba. .”
Sanusi Bature Dawakin Tofa mai magana da yawun gwamna Abba Kabir Yusuf, ya shaidawa BBC cewa wannan kira da shugaban APC ya yi musu a kwararo suka ji shi.
”Mun ji bayyanin cewa ya miko wannan ƙoƙon bara na gwamna ya dawo jam’iyyar APC to amma abin mamaki shi ne, shi Ganduje a matsayinsa na tsohon gwamna da tsohon mataimakin gwamna ya fi kowa sanin hanyar da ake isarwa gwamna mai ci sako idan ana son ya je wurinsa”, in ji Sanusi.
Ya kuma kara cewa gwamna Yusuf ba shi da wata matsaya ta barin jam’iyyarsa ko kin barin jam’iyyarsa.
”Amma maganar da muka ji ya faɗa a kafafen yaɗa labarai na zumunta mu ka ji ta kuma a nan mu ka barta’’
”Ka san ita siyasa ko in ce sauya sheka ta siyasa kamar canza gida ne, ba ka tashi lokaci ɗaya kawai ka dauki jakarka ka fita, ka ce wai ka canja gida.
“Akwai abubuwan da za ka iya yi kafin ka ce ka canja gida saboda don haka mu a wurinmu wannan sako mun ji ne kawai kamar a sama”, in ji shi.
Wannan yunkuri na jam’iyyar APC na zuwa ne bayan umarni da shugaba Tinubu ya bayar, na cewa ɓangarorin biyu su je su sasanta da juna.
Wasu dai na ganin cewa abu ne mai matuƙar wuya waɗannan ɓangarori su iya ajiye rigingimun da ke tsakaninsu su yi aiki tare idan ta tabbata cewa za su haɗe, musamman kan wanda zai zama jagora.
