Connect with us

Business

Ragewa Da Kara Farashin Man Fetur Da Matatar Man Dangote Ke Yi Ka Iya Jefa Nigeria cikin Masharsharar Tattalin Arziki —Yan Kasuwa

Published

on

Screenshot 20260131 161951 768x500
Spread the love

Masu harkar sayar da man fetur a Najeriya, tare da masana harkar makamashi, masu sa ido da ƙungiyoyin ƙwadago, sun bayyana damuwa kan yadda ake fama da rashin tabbas na ragewa da kara farashin man fetur da kuma  rarraba sa a ƙasar.

Sun ce wannan yanayi na haifar da fargaba a kasuwar man fetur, musamman ganin yadda farashi ke sauyawa ba tare da wani  tabbatacce ba, lamarin da ke jefa ’yan kasuwa da masu amfani da mai cikin ruɗani.

Gwamnatin Ta Haramta Chaba Kwalliyar Fuska Ga Mata Ma’aikata A Ofisoshi

Masu sa ido sun danganta matsalar da tsarin aikin da Matatar Dangote ke bi, musamman tsarin da ake kira single train.

Advertisement

Sun yi gargadin cewa idan ba a dauki matakin gaggawa ba, hakan na iya yin mummunan tasiri ga tattalin arzikin Najeriya.

Da suke zantawa da manema labarai, wasu daga cikin masu sayar da man fetur sun ce yadda matatar ke aiki da tsarin ragewa da kara farashin man fetur a halin yanzu bai yi dai-dai da tanade-tanaden dokar Petroleum Industry Act (PIA) ba, dokar da aka kafa domin tsara harkar man fetur da gas a Najeriya.

A cewarsu, hakan na iya girgiza tsarin samar da man fetur, tare da jefa kasuwa cikin wani hali.

Masu sayar da mai masu zaman kansu sun ce a kwanakin baya farashin man fetur daga matatar, wato farashin da ake sayarwa ga ’yan kasuwa kafin ya isa gidajen mai, ya tashi daga naira ₦699 zuwa ₦799.

Advertisement

Haka kuma, sun ce farashin da jama’a ke siya a gidajen mai ya rika canzawa daga naira ₦731 zuwa kusan ₦920 cikin ɗan gajeren lokaci.

Sun bayyana wannan yanayi a matsayin sauyin farashi mara tabbas, wanda ke jefa ’yan kasuwa da masu amfani da man fetur cikin matsin lamba.

Wasu masana harkar makamashi sun kuma zargi Matatar Dangote da aiwatar da dabarun kasuwanci da ke takura masu  shiga harkar, inda suka ce hakan na iya hana wasu kamfanoni shiga kasuwar man fetur a Najeriya.

A cewarsu, idan kamfani guda ya rinjayi kasuwa fiye da kima, hakan na iya hana zuba jari, haddasa rikicin farashi, tare da barazana ga dorewar bangaren man fetur baki ɗaya.

Advertisement

“Man fetur na da tasiri kai tsaye ga tattalin arzikin kasa, domin duk wani sauyi a farashinsa na shafar farashin sufuri, abinci da sauran kayayyaki.

Idan ba a aiwatar da dokokin Kasuwa yadda ya kamata ba, tattalin arziki na iya shiga mawuyacin hali,” in ji masu sa idon.

Sun kuma bayyana cewa Matatar Dangote, wacce ke da karfin tace ganga 650,000 na danyen mai a rana, na aiki ne da layin tacewa guda daya kacal.

A cewarsu, wannan na nufin dukkan samar da man fetur na rataye ne kan tsari guda, wanda ke iya tsayawa gaba ɗaya idan aka samu matsala ta fasaha.

Advertisement

Sun ce rahotanni sun nuna cewa wani muhimmin sashen matatar, wanda ke taimakawa wajen tace man fetur mai inganci, ya fuskanci tsaiko, abin da ke kara nuna hadarin dogaro da tsari guda.

Masu sa idon sun kara da cewa Najeriya na bukatar kusan lita miliyan 70 na man fetur a kowace rana, kamar yadda hukumar da ke kula da harkar man fetur ta kasa ta bayyana, amma a halin yanzu ana samar da kasa da rabin wannan adadi.

Kungiyoyin ƙwadago sun bukaci gwamnatin tarayya da Majalisar Dokoki ta kasa da su tabbatar da cikakken aiwatar da dokar PIA, suna mai cewa an kafa dokar ne domin tabbatar da adalci da daidaito a masana’antar man fetur.

Sun kuma yi gargadin cewa idan ba a samar da gaskiya a ragewa da kara farashin man fetur da kuma hanyoyin aiki ba, Najeriya na iya fuskantar matsalar makamashi da za ta yi tasiri kai tsaye ga rayuwar al’umma da tattalin arzikin kasa.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *