Connect with us

News

Gwamnatin Ta Haramta Chaba Kwalliyar Fuska Ga Mata Ma’aikata A Ofisoshi

Published

on

A Op8T43y9nK 2026 01 29 1769679759resized pic
Spread the love

Gwamnatin jihar Laziqiyyah da ke ƙasar Siriya ta haramta wa mata ma’aikatan gwamnati chaba kwalliyar fuska yayin lokutan aiki a ofisoshi da ma’aikatun gwamnati, matakin da ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin jama’a.

Hukumomin jihar sun bayyana cewa an dauki matakin ne domin tsara Samar da dai dai to ga ma’aikata da kiyaye martabar ofisoshin gwamnati, suna mai cewa ba wai don takaita ‘yancin mata ko keta hakkokinsu ba ne.

Wasu Gungun Fusatattun Matasa Sun Bankawa Barawon Waya Wuta A Dorayi

Advertisement

Sai dai masu fafutukar kare haƙƙin ɗan Adam sun soki umarnin, inda suka ce yana nuna katsalandan a rayuwar mata ta kashin kai da kuma karkatar da hankali daga manyan matsalolin da ke addabar kasar.

‎Wata ma’aikaciyar gwamnati mai suna Nadine ta ce matakin ya bata mata rai, tana mai cewa Chaba Kwalliyar Fuska ba ta taba zama ma’aunin kwarewa ko jajircewa wajen aiki ba.

Rahotanni sun nuna cewa wannan ba shi ne karon farko da irin wadannan matakai ke janyo ce-ce-ku-ce a jihar Laziqiyyah ba, inda a baya ma aka fitar da umarnin da ya shafi tufafin mata a wuraren shakatawa.

Advertisement

 

 

THE NEW ARAB

Advertisement
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *