News
Wasu Gungun Fusatattun Matasa Sun Bankawa Barawon Waya Wuta A Dorayi
DAGA UMAR IBRAHIM MUHD
Wasu gungun fusatattun matasa a unguwar Dorayi, karshen Waya, dake jihar Kano Sun bankawa wani da ake zargin Barawon Waya ne wuta bayan da ya yi yunkurin kwace wayar wata mata.
Rahotanni sun ce barawon ya cika matar wuka a kirjin ta kafin matasan su yi masa ramuwar gayya.
Wasu Gungun Fusatattun Matasa Sun Bankawa Barawon Waya Wuta A Dorayi
An garzaya da matar zuwa asibiti domin samun kulawar gaggawa daga likitoci, yayin da jami’an tsaro suka iso wurin suka dauki barawon domin gudanar da bincike.
Har yanzu, hukumar ‘yan sanda ba ta fitar da wani bayani kan lamarin ba,
Lamarin ya janyo cece-kuce a tsakanin mazauna yankin, musamman game da yadda matasa ke daukar matakan kare kansu daga miyagun laifuka.
