Connect with us

News

Zazzabin Lassa Ya Yi Ajalin Mutum 17 A Jihohi 8  — Hukumar NCDC

Published

on

Lafiya

Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa NCDC ta bayyana cewa a cikin makonni uku na shekarar 2026 zazzabin lassa ta yi ajalin mutum 17 a jihohi 8 a kasar nan.

Bisa ga sanarwan mako-mako da hukumar ke fitarwa a shafinta na yanar gizo ya nuna cewa a mako na uku na yaduwar cutar jihohin Bauchi, Taraba, Filato, Ondo, Edo, Ebonyi, Benuwe da Nasarawa sun samu kashi 46% a yaduwar cutar.

Advertisement

Ragewa Da Kara Farashin Man Fetur Da Matatar Man Dangote Ke Yi Ka Iya Jefa Nigeria cikin Masharsharar Tattalin Arziki —Yan Kasuwa

Hukumar ta ce daga wadannan jihohi an samu mutum 93 da aka tabbatar sun kamu da cutar.

Advertisement

Zuwa yanzu yaduwar cutar a 2026 ya kai kashi 18.1% Kasa da kashi 18.2% din da aka samu a 2025 a irin wannan lokaci.

NCDC ta ce jami’an lafiya hudu sun kamu da cutar a cikin mako na uku na yaduwar cutar.

Advertisement

Hukumar ta ce kashi 89% na mutanen da suka kamu da cutar an gano su ne daga jihohin Bauchi, Ondo, Taraba da Edo.

Matasa masu shekaru 21 zuwa 30 na daga cikin rukunin mutanen da suka fi kamuwa da cutar sannan maza sun fi mata kamuwa da cutar.

Advertisement

Har ya zu dai rashin sani, rashin zuwa asibiti da rashin tsaftace muhalli na daga cikin matsalolin dake ci gaba da yada cutar.

Gwamnati ta ce za ta ci gaba da kokari musamman ta hanyar daukan matakan da suka fi dacewa domin dakile yaduwar cutar.

Advertisement

 

 

Advertisement

PREMIUM TIMES

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending