Connect with us

News

Kotu Ta Yanke Wa Shugaban Kamfani Hukuncin Daurin Shekaru 48 Kan Damfarar Fiye Da Mutum 5,000 ‎

Published

on

IMG 20260204 063207 307
Spread the love

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Makurdi, a Jihar Benue, ta yanke wa Manajan Daraktan kamfanin Builderstech Solution Ltd, Agene Johnson Godwin, hukuncin daurin shekaru 48 a gidan yari bisa samun sa da laifin damfarar jama’a fiye da mutum 5,000.

‎Mai shari’a M.S. Abubakar ya yanke hukuncin ne bayan kotu ta same shi da laifi a kan zarge-zarge takwas da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta shigar a kansa.

Shekaru 50: Yadda Janar Murtala Muhammad Ya Sauya Taswirar Najeriya Da Ƙirƙiro Sabbin Jihohi

‎Kotun ta saurari cewa wanda aka yanke wa hukuncin ya karɓi kuɗaɗe daga jama’a ta hanyar shirin saka jari na bogi a ƙarƙashin kamfanin Builderstech Solution Ltd, inda aka ce ya yi awon gaba da sama da Naira miliyan 500.

Advertisement

‎An bayyana cewa Godwin ya yaudari masu zuba jari ne da alkawarin riba mai yawa da ba ta dace da gaskiya ba, abin da ya jawo asarar kuɗi ga dubban mutane.

‎Bayan yanke hukuncin, kotun ta ce an yi hakan ne ba tare da zaɓin tara ba, la’akari da girman laifin da yawan mutanen da abin ya shafa.

‎A nata ɓangaren, EFCC ta sake jan hankalin ‘yan Najeriya da su yi taka-tsan-tsan wajen saka jari, musamman a shirye-shiryen da ke yin alkawarin riba fiye da kima.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *