News
Shekaru 50: Yadda Janar Murtala Muhammad Ya Sauya Taswirar Najeriya Da Ƙirƙiro Sabbin Jihohi
A Ranar Talata ake cika shekaru 50 cif da gwamnatin mulkin sojin Najeriya karkashin marigayi Janar Murtala Ramat Muhammad ta sanar da ƙirƙiro sabbin jihohi a ƙasar, matakin da masana ke cewa ya yi tasiri mai zurfi ga tsarin mulki da tafiyar da Najeriya.
A ranar 3 ga Fabrairu, 1976, gwamnatin sojin ta ƙara jihohi bakwai—wato Bauchi, Benue, Borno, Imo, Niger, Ogun da Ondo—lamarin da ya kai adadin jihohin Najeriya daga 12 zuwa 19.
Gwamnatin Tarayya Na Duba Yiwuwar Raba Tallafin Wutar Lantarki Da Jihohi Da Ke Bukatar Rangwame
Masana tarihi sun bayyana cewa ƙirƙiro jihohin ya taimaka wajen kusantar da gwamnati ga al’umma, tare da rage cunkoson iko da kuma bai wa yankuna dama wajen tafiyar da harkokinsu na siyasa da tattalin arziƙi.
Duk da cewa mulkinsa bai daɗe ba, sakamakon kisan gillar da aka yi masa a juyin mulkin 13 ga Fabrairu, 1976, ana ci gaba da tuna Janar Murtala Muhammad a matsayin shugaba da ya aiwatar da manyan sauye-sauye a Najeriya.
Jihar Bauchi Na Cika Shekaru 50
Jihar Bauchi na daga cikin jihohin da aka ƙirƙiro a shekarar 1976, bayan da aka ware ta daga babbar Jihar Arewa maso Gabas, mai hedikwata a Maiduguri.
Tun daga kafuwarta, jihar ta yi gwamnoni 16, inda wasu suka shugabanci a lokacin soja, yayin da wasu kuma suka hau mulki ta hanyar dimokuradiyya.
Domin tunawa da wannan rana, gwamnatin jihar Bauchi ta ayyana hutun aiki ga ma’aikata, yayin da gwamnan jihar, Sanata Bala Abdulkadir Muhammad, ya yi jawabi na musamman domin jinjinawa masu fafutukar samar da jihar. Har ila yau, an sanar da sauya sunan Unity Park zuwa Unity Jubilee Park.
A tsawon rabin ƙarni, jihar Bauchi ta fuskanci nasarori da ƙalubale da dama. Duk da haka, ana ci gaba da kallonta a matsayin ɗaya daga cikin jihohin da aka san su da zaman lafiya a Arewa maso Gabashin Najeriya.
