News
Gwamnatin Tarayya Na Duba Yiwuwar Raba Tallafin Wutar Lantarki Da Jihohi Da Ke Bukatar Rangwame
Gwamnatin Tarayyar Najeriya na nazarin sauya tsarin tallafin wutar lantarki, inda ta bayyana shirin raba nauyin tallafin da jihohin kasar, musamman wadanda ke neman rangwame domin rage tsadar wutar da al’ummarsu ke fuskanta.
Matakin, wanda ke zuwa a daidai lokacin da ake fama da matsin tattalin arziki, na iya kawo sauyi mai girma ga bangaren wutar lantarki a kasar, tare da janyo damuwa ga masu ruwa da tsaki da kuma al’ummar karkara da ke cin gajiyar tsarin tallafin a halin yanzu.
An Kashe Saif Al-islam Ɗan Tsohon Shugaban Libya Mu’ammar Gaddafi
A karkashin tsarin da ake amfani da shi, masu amfani da wuta a birane na daukar wani bangare na tsadar wutar domin rage nauyi ga al’ummomin karkara. Gwamnatin Tarayya ta ce tana kashe kusan Naira tiriliyan biyu a duk shekara wajen tallafa wa wutar lantarki, kudin da ta ce ya zama mai nauyi ga kasafin kudin kasa.
Sai dai tun daga farkon shekarar nan, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ba za ta iya ci gaba da daukar nauyin tallafin ita kadai ba, sakamakon karuwar basussuka da kuma bukatar daidaita harkokin kudi. A cewar bayanai daga hukumomin kasafin kudi, ana duba tsarin da zai bai wa jihohi damar daukar wani bangare na nauyin tallafin wutar lantarki a yankunansu.
Masu sharhi na ganin cewa wannan sauyi na iya kaiwa ga karin kudin wutar lantarki, musamman a yankunan karkara, inda wuta ke zama muhimmin ginshiki ga kananan sana’o’i da rayuwar yau da kullum. A halin yanzu, wutar lantarki ita ce kadai manyan ayyukan gwamnati da har yanzu ke samun tallafi, bayan janye tallafin man fetur da rage shiga kai tsaye a wasu sassan tattalin arziki.
A karkashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Najeriya na aiwatar da jerin manufofin sauyi da suka shafi rage tallafi, matakan da ke fuskantar suka daga kungiyoyin kwadago da masana, musamman ganin cewa albashin ma’aikata bai yi daidai da hauhawar farashin kayayyaki ba.
Masana tattalin arziki sun yi gargadin cewa rage ko janye tallafin wutar lantarki a yankunan karkara na iya illata tattalin arzikin karkara.
