News
An Kashe Saif Al-islam Ɗan Tsohon Shugaban Libya Mu’ammar Gaddafi
Rahotanni daga ƙasar Libya sun ce wasu mutane da ba’a iya tantancewa ba suka hallaka ɗan Mu’ammar Gaddafi tsohon shugaban ƙasar Saif-al-Islam, bayan sun buɗe masa wuta a yammacin ƙasar.
Lauyan sa Khaled el-Zaydi ya tabbatar da kisan ga manema labarai a yau Talata, duk da ya ke babu cikakken bayani a kan dalilan da suka haddasa kisan.
An Kwashe Sama Da Mutum 200 Masu Larurar Kwakwalwa Daga Tituna — Gwamnatin Kano
Ɗan tsohon shugaban ya kwashe shekaru ya na zama a matsayin wanda zai gaji mahaifinsa, kafin lokacin da aka kama shi aka tsare da kuma lokacin da ya kuɓuta zuwa lokacin da ya nemi tsayawa takarar shugabancin Libya.
Duk da ya ke ba shi da wani muƙami na gwamnati, ya kasance ana kallon sa a matsayin mai karfin faɗa a ji a ƙasar da mahaifinsa ya kwashe shekaru sama da 40 yana jagoranci.
Saif al-Islam ya bada gudumawa wajen tsara manufofi masu girma da kuma harkokin diflomasiyar ƙasar, yayin da ya kuma jagoranci tattaunawar watsi da shirin nukiliyar Libya da biyan diyya ga iyalan mutanen da suka mutu a haɗarin jirgin Pan Am da ya faɗi a Lokerbie Scotland a shekarar 1988.
A ƙoƙarin sa na sauya makomar Libya wadda duniya ta juyawa baya, Saif al-Islam ya rungumi tattaunawa da ƙasashen Yammacin duniya da kuma gabatar da kansa a matsayin ɗan neman sauyi, tare da gabatar da buƙatar sauya kundin tsarin mulkin Libya da kuma kare hakkin Bil Adama.
Marigayin ya yi karatu ne a Cibiyar Tattalin Arziki ta London kuma ya samu karɓuwa a wurn gwamnatocin ƙasashen yamma, amma lokacin da aka kaddamar da juyin juya hali domin kawar da mahaifinsa a shekarar 2011, sai ya jagoranci kafa wata runduna ta kabilanci domin dirar mikiya a kan masu yi wa mahaifinsa bore da ya bayyana su a matsayin ɓeraye.
Bayan da masu zanga zanga suka kwace birnin Tripoli, Saif al-Islam ya nemi mafaka a Jamhuriyar Nijar, yayin da bangaren Abu Bakr Sadik na ƴan tawayen ƙasar suka kama shi inda suka kai shi suka tsare a birnin Zintan.
Marigayin ya kwashe shekaru 6 yana tsare a Zintan, yayin da daga bisani aka masa shari’a tare da yanke masa hukuncin kisa a Tripoli.
Saif ya kwashe shekaru yana tsare a ƙarƙashin kasa kafin sakin sa a shekarar 2017 a ƙarƙashin shirin AmnestyAmnesty.
A shekarar 2021, Saif ya gabatar da takardun sa na neman tsayawa takarar shugabancin ƙasar, amma aka soke takarar ta sa saboda rawar da ya taka a rikicin shekarar 2015.
