News
Shari’ar gwamna: Al’umma da dama sun shiga rudani a jihar kano sakamakon fitar hukuncin kotun daukaka kara
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Al’umma da dama sun shiga rudani a jihar kano sakamakon fitar hukuncin kotun daukaka kara da ta yanke a ranar juma’a 17 ga watan Nuwamba 2023, wanda a cikin sa ta tabbatar da hukuncin da kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan jihar kano ta na soke nasarar Abba Kabir Yusuf, tare da tabbatar da cewa Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ne ya lashe zaben gwamnan jihar..
Rudanin dai ya samu asalin ne lokacin da mutane suka fahimci cewa a cikin wani bangare na hukuncin kotun daukaka kara, ta ce Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP ne ya yi nasara a Shari’ar Kuma har aka umarci daya ɓangaren da ya biya Abba Kabir tarar Naira Miliyan guda, sabanin abun da kotun ta fada a ranar yanke hukuncin .
Hakan yasa magoya bayan jam’iyyar NNPP da kwankwasiyya suke ta sowa tare fadin dama kuskure aka samu wajen karanta hukuncin, wasu kuma suke cewa Allah ne ya fito da abun da aka rufe.
Hukumar tace Fina-finai ta Kano ta Bayyana Dalilan Dakatar da Jaruma Khadija Mai Numfashi
Sai dai lauyoyin dukkanin bangarorin biyu sun fito sun yiwa al’umma karin haske kan yadda lamarin yake.
Barr. Jamil SAN na daga cikin lauyoyin jam’iyyar APC yace kuskure ne aka samu wajen rubuta hukuncin amma hakan ba zai chanza hukuncin da kotun daukaka karar ta yanke ba.
Shi ma Barr. Abba Hikima Fagge wanda wasu suke yi masa kallon dan jam’iyyar NNPP ya fito karar ya bayyana cewa kuskure ne aka samu wajen rubuta hukuncin, wanda kuma dama an saba ganin irin wadancan kura-kuran a mafi yawan hukunce-hunkuce da Kotuna suke yi.
Yace ” A harkar hukuncin kotu ba’a daukar wani bangare guda na hukunci a dora da shi , dole sai an yi la’akari da sauran bangarorin hukuncin, don haka ya tabbatar da cewa kuskure da aka samu ba zai chanza hukuncin da kotun daukaka karar ta yanke ba.
Har yanzu dai a hukumance duk cikin wadanda suke cikin Shari’ar babu wanda ta fito yace komai dangane da wannan sabuwar dambarwa.
