Connect with us

News

Kungiyar Izala Ta Dakatar Da Sheikh Alkali Zaria Daga Cigaba Da Gabatar Da Tafsiri A Wannan Watan Na Azumi

Published

on

YKklKZRZecJ1uxxxePzQdwWxzXhA0O0YF8KBUuts
Spread the love

Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) mai hedikwata a Jos ta sanar da dakatar da Sheikh Alkali Abubakar Salihu Zaria daga ci gaba da gabatar da tafsiri a Damaturu, bisa dalilan tsaro da kuma abin da ta kira saɓawa ƙa’idojin ƙungiyar.

A cikin sanarwar da reshen ƙungiyar ya fitar, an bayyana cewa an turo malamin ne daga hedikwatar ƙasa kamar yadda aka saba yi tsawon shekaru 35, kuma ya fara tafsiri na watan Ramadan har tsawon kwanaki sha ɗaya kafin a dakatar da shi a ranar 12 ga Ramadan.

Gwamnatin Tarayya Ta Tara Fiye Da Naira Tiriliyan Biyu Daga Harajin VAT A Cikin Wata Uku  —NBS

Advertisement

Sanarwar ta ce shugaban Majalisar Malamai ta ƙasa, Muhammad Sani Yahya Jingir, ne ya bayar da umarnin dakatarwar bayan wasu hudubobi da nasihohi da malamin ya gabatar, ciki har da wa’azin da ya yi a Hedikwatar ’Yan Sandan Jihar Yobe da kuma wasu wurare a Damaturu.

Ƙungiyar ta ce salon wa’azin da ya haɗa da ambaton sunayen mutane da kalaman da ta bayyana a matsayin tsinuwa da jafa’i ya saɓa da tsarin koyarwar Izala. Ta kuma ce kalaman sun shafi sassa daban-daban na al’umma, ciki har da jami’an tsaro da shugabanni.

A ranar 14 ga Ramadan 1447, an kira malamin tare da wasu shugabanni a wani zama, inda aka saurari bayanansa kafin a yanke shawarar janye shi daga Damaturu.

Advertisement

A cewar sanarwar, Sheikh Alkali ya amince da kuskurensa tare da bayar da haƙuri ga shugabannin ƙungiyar da al’umma baki ɗaya, yana mai fatan Allah Ya gafarta kura-kurai.

 

AMMASCO RADIO 

Advertisement
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *