Connect with us

News

Wani Mutum Ya Kashe  Ɗan’uwansa Bisa Tunanin  A Mafarki Ne 

Published

on

Yan sanda sun cafke wani ango a ranar ɗaurin aurensa kan zargin kisan kai

‎Rundunar ’yansandan Jihar Oyo a kudu maso yammacin Najeriya ta sanar da kama wani mutum mai shekaru 43 bisa zargin hallaka babban ɗan’uwansa, bayan ya yi ikirarin cewa marigayin ya harbe shi a mafarki.

Lamarin ya faru ne a garin Sepeteri, inda ake zargin Lateef Suleiman ya kai hari kan ɗan’uwansa mai shekaru 52, Mustapha Amidu.

Advertisement

Kungiyar Izala Ta Dakatar Da Sheikh Alkali Zaria Daga Cigaba Da Gabatar Da Tafsiri A Wannan Watan Na Azumi

‎A wata sanarwa da kakakin rundunar ’yansandan jihar, DSP Ayanlade Olayinka, ya fitar, ya ce wanda ake zargin ya farka daga barci cikin tashin hankali, yana mai zargin cewa ɗan’uwansa ya harbe shi a mafarki.

Advertisement

‎Rahotanni sun ce bayan farkawarsa, ya nufi inda marigayin yake, ya ɗauki wani babban dutse ya buge shi a kai, kafin daga bisani ya tsere daga wurin.

‎An garzaya da wanda aka kai wa harin zuwa asibitin Ileri Oluwa Hospital, amma likitoci sun tabbatar da rasuwarsa sakamakon munanan raunukan da ya samu.

Advertisement

‎Jami’an ’yan sanda daga hedikwatar Ago-Amodu sun kai ziyara wurin da abin ya faru domin gudanar da binciken farko, kafin daga bisani su cafke wanda ake zargin.

‎Rundunar ta ce mutumin ya amsa laifin da ake zarginsa da shi, kuma yana ba da hadin kai wajen bincike.

Advertisement

‎Kwamishinan ’yan sandan jihar, Femi Haruna, ya bayar da umarnin mika karar zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na rundunar (SCID) domin ci gaba da zurfafa bincike tare da daukar matakan doka da suka dace.

‎’Yan sanda sun kuma yi kira ga al’umma da su kauce wa daukar doka a hannunsu, tare da neman mafita ta hanyar bin ka’idojin doka.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending