Connect with us

News

Jami’an NSCDC Sun Cafke Wani Da Ake Zargi Da Safarar Bindigogi A Kano ‎

Published

on

IMG 20260304 WA00262

Jami’an Nigeria Security and Civil Defence Corps (NSCDC) reshen Jihar Kano sun kama wani mutum da ake zargi da safarar makamai ba bisa ka’ida ba, yayin wani samame da suka kai a kan titin Murtala Muhammad Way a birnin Kano.

‎A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce an cafke wanda ake zargin ne mai suna Suleiman M. Uba, mai shekaru 31, dan asalin kauyen Tashene da ke karamar hukumar Zaki a Jihar Bauchi.

Advertisement

Wani Mutum Ya Kashe  Ɗan’uwansa Bisa Tunanin  A Mafarki Ne 

‎Sanarwar ta kara da cewa ana zargin mutumin na kan hanyarsa ta zuwa Jihar Kebbi ne a lokacin da jami’an suka tare shi domin bincike.

Advertisement

‎Binciken farko, a cewar rundunar, ya nuna cewa an same shi dauke da bindigogi guda shida. Jami’an sun ce kamen ya biyo bayan sahihan bayanan sirri da suka samu, a wani mataki na kokarin dakile yaduwar kananan makamai da kuma hana ayyukan da ka iya tayar da zaune tsaye a Kano da makwabtanta.

‎Rundunar ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, tare da tabbatar da cewa za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala binciken.

Advertisement

 

 

Advertisement

DAILY NIGERIAN 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending