News
Iftila’in Gobara Ya Yi Ajalin Mutum 128
An shiga alhini a Hong Kong a wannan Asabar, a yayin da cincirindon jama’a suka fito don nuna girmamawa tare da ajiye furanni ga mutane 128 da suka mutu a ɗaya daga cikin iftila’in gobara mafi muni a birnin, lamarin da ke alamta fara zaman makoki na kwanaki uku a hukumance.
Ɗimbim jama’a daga sassan ƙasar ne suka hallara a wani dandali na kusa da benayen Wang Fuk, wadanda suka shafe tsawon sa’o’ 40 su na ci da wuta, domin ajiye furanni da sakwannin ta’aziyya.
Kuskure Ne Tattaunawa Da Ƴan Bindiga A Najeriya —Olusegun Obasanjo
A wani wuri a yankin Tai Po, wani ɗakin taro ne aka mayar da shi cibiyar karɓar saƙwannin ta’aziyya, inda jama’a za su riƙa zuwa tsawon waɗannan kwanaki uku.
A yayin wannan zaman makoki, za a soke ko kuma dakatar da dukkannin bukukuwa da aka tsara yi, kana jami’an gwamnati za su rage fita bainar jama’a da suka tsara yi musamman ma idan ba masu mahimmanci ba ne.
Jagran birnin Hong Kong John Lee da manyan ministocinsa sun yi tsayuwar shuru na mintina 3 da misalin ƙarfe 8 na safe a wajen shelkwatar gwamnati, inda aka yi ƙasa-ƙasa da tutocin China da na Hong Kong.
Ƴansanda sun fada a wannan Asabar cewa adadin waɗanda suka mutu na nan a 128, kana shuka shiada wa wani taron manema labarai cewa har yanzu akwai wasu gawarwaki 44 da ke jira a shaida masu su.
Har yanzu masu aikin ceto na ta ƙoƙarin laluɓen kimanin mutane 150 da aka ce sun ɓace ko kuma an rasa sduk wata hanyar saduwa da su.
