Connect with us

News

Gwamnan Kano ya sauke shugaban ma’aikatan jihar Alhaji Abdullahi Musa daga mukaminsa

Published

on

FB IMG 1773180669753

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sauke Shugaban Ma’aikatan Jihar, Abdullahi Musa, daga mukaminsa nan take.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na Gidan Gwamnatin Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar.

Advertisement

Lauyoyin Gwamnatin Kano Sun Shirya Tsunduma Yajin Aiki A Fadin Jihar 

Sanarwar ta ce matakin wani bangare ne na kokarin gwamnatin jihar na sake farfado da tsarin aikin gwamnati domin inganta kwarewa, ladabi da kuma kyakkyawan gudanar da ayyuka a hukumomin gwamnati.

Advertisement

Gwamnan ya gode wa tsohon Shugaban Ma’aikatan Jihar bisa gudunmawar da ya bayar wajen hidimtawa jihar Kano tare da yi masa fatan alheri a rayuwarsa ta gaba.

Hakazalika, an umarci Bilkisu Shehu Maimota, Babbar Sakatariya mai kula da Harkokin Gudanarwa da Ayyuka na Ofishin Majalisar Zartarwa, da ta rike mukamin Shugaban Ma’aikatan Jihar na rikon kwarya har sai an nada wanda zai rike mukamin na dindindin.

Advertisement

Sanarwar ta kuma umarci tsohon Shugaban Ma’aikatan Jihar da ya mika ragamar ofishin ga wacce za ta rike mukamin na rikon kwarya kafin ko a ranar Laraba, 11 ga Maris, 2026.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending