Sports
Real Madrid ta naɗa Álvaro Arbeloa domin maye gurbin Alonso
Ƙungiyar Real Madrid ta sanar da naɗa tsohon ɗan’wasanta Álvaro Arbeloa a matsayin sabon kocinta domin maye gurbin Xavi Alonso.
Álvaro Arbeloa tsohon ɗanwasan ƙasar Spain ne da Real Madrid, inda ya kasance yana buga baya.
EFCC Ta Saka Naira Bliyan 3.2 Don Tsaftace Ofisoshinta Da Kayan Makwalashe A Kasafin Kuɗin 2026
Kafin naɗa shi wannan matsayin, shi ne mai horas da matasan ƴanwasan ƙungiyar.
Kwana ɗaya bayan Barca ta doke ta a gasar Spanish Super Cup, Real Madrid ta sanar da rabuwa da kocinta Xabi Alonso tare da naɗa Alvaro Arbeloa.
Alonso ya kwashe kusan wata bakwai yana horar da tawagar bayan maye gurbin Carlo Ancelotti.
