News
Mahukunta A Nijar Sun Haramta Fitar Da Dabbobi Daga Kasar Zuwa Kasashen Ketare
Mahukunta a Jamhuriyar Nijar sun sanar da haramta fitar da dabbobi zuwa kasashen ketare, a wani mataki da gwamnatin kasar ta ce an dauka domin rage tashin farashin dabbobi a cikin gida.
Sanarwar da hukumomin kasar suka fitar ta nuna cewa matakin na daga cikin kokarin da gwamnati ke yi na daidaita farashin kayayyaki da kuma tabbatar da cewa al’umma na samun dabbobi cikin sauki.
An Kama Jami’an Gwamnatin Ghana 9 Da Kwantena Dauke Kwayoyin Tramadol
Wannan dai ba shi ne karo na farko da gwamnatin Nijar ke daukar irin wannan mataki ba. A bara ma hukumomin kasar sun ayyana irin wannan doka domin dakile tashin farashin dabbobi da ake fitarwa zuwa wasu kasashen makwabta.
Sai dai matakin ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin masu sana’ar saye da sayar da dabbobi. Wasu daga cikin ‘yan kasuwar da masu safarar dabbobin sun nuna rashin jin dadinsu, inda suka ce dokar ka iya janyo musu asarar kudaden shiga.
A gefe guda kuma, wasu daga cikin al’ummar kasar sun nuna goyon bayansu ga matakin, suna masu cewa hakan zai taimaka wajen rage tsadar dabbobi a kasuwannin cikin gida.
Nijar na daga cikin kasashen da ke da dimbin dabbobi a yankin Sahel, kuma ana yawan fitar da su zuwa kasashe makwabta da ke yankin Yammacin Afirka.
