Connect with us

News

RIKICIN GABAS TA TSAKIYA: Akwai Yiwuwar Samun Karancin Magunguna A Najeriya

Published

on

images (2)
Advertisements
Advertisements
Spread the love

Masu ruwa da tsaki a bangaren hada da rarraba magunguna sun yi gargadin cewa rikicin da ke kara kamari a yankin Gabas ta Tsakiya na iya janyo karancin magunguna a Najeriya, idan har ba a samu saukin lamarin ba cikin gaggawa.

A cewarsu, rikicin da ya shafi Iran da wasu kasashe na yankin na barazana ga tsarin kasuwanci da safarar kayayyaki na duniya, musamman ma a bangaren magunguna.

Kotu A Amurka Ta Soke Matakin Trump Na Rufe VOA

Advertisement

Rahotanni sun nuna cewa fiye da kashi 70 cikin 100 na magungunan da ake amfani da su a Najeriya ana shigo da su ne daga kasashen waje, musamman India da China. Wannan na nufin duk wata tangarda a harkokin sufuri da kasuwanci na iya jefa kasar cikin matsala.

Haka kuma, masana sun bayyana cewa rikicin na iya shafar shirye-shiryen tallafin kiwon lafiya da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa, ciki har da yakar cututtuka irin su HIV/AIDS, tarin fuka da kuma malaria, baya ga kula da lafiyar mata da kananan yara.

Bugu da kari, fargabar katsewar safarar danyen mai ta mashigar Strait of Hormuz na kara jefa damuwa a kasuwannin duniya, lamarin da ka iya haifar da tsaiko a jigilar kayayyaki, ciki har da magunguna.

Advertisement

Masu sa ido kan al’amuran tattalin arziki sun ce idan rikicin ya ci gaba da tsananta, kasashen da ke dogaro da shigo da magunguna, ciki har da Najeriya, na iya fuskantar matsalar karanci, wanda zai iya yin illa ga lafiyar al’umma.

 

 

Advertisement

DW

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending