Connect with us

News

An Kama Matasa 3  Bisa Zargin Yunkurin Kashe ’Yan Bijilante A Kano  ‎

Published

on

Advertisements
Advertisements
Spread the love

Rundunar tsaro ta Anti-Phone Snaching Force dake Kano, wacce ke yaki da fadan daba, kwacen waya da kuma dakile ta’ammali da kayan maye, ta kama wasu matasa uku bisa zargin yunkurin kashe jami’an kungiyar sintirin Bijilante uku a Bechi Gunkawa, karamar hukumar Kumbotso.

‎Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Ibrahim Garba Ahmad, ya bayyana haka yayin zantawarsa da gidan rediyon Dala FM a ranar Lahadi, 22 ga watan Maris, 2026.

Gwamnatin Kano Ta Nuna Damuwa Kan Karancin Komawar Dalibai Makarantu Bayan Kammala Hutun Sallah

Advertisement

‎Ibrahim Garba ya ce, daga cikin matasan da aka kama, Shu’aibu Muhammad, mai shekaru 20, an zarge shi da dukan mahaifinsa yayin da rikici ya barke tsakanin iyayensa a gida, inda ya shiga cikin fada tsakanin mahaifinsa da mahaifiyarsa.

‎“Bayan faruwar hakan ne Malam Muhammad, mahaifinsa, ya kai rahoto ga jami’an Bijilante na yankin Bechi Gunkawa, inda suka yi masa ladabtarwa. Daga baya, matashin da abokansa huɗu suka nufi gidan ’yan Bijilante dauke da makamai, suna barazanar kashe su. Sai dai, basu samu nasarar aikata hakan ba, kafin jami’an tsaro su kama su,” in ji Ibrahim Garba Ahmad.

‎Ya kara da cewa, yayin samame, daya daga cikin matasan ya tsere, amma aka kama sauran uku ciki har da jagoran tawagar, wadanda suka amsa laifukan da ake zargin su da aikatawa.

Advertisement

‎Daya daga cikin jami’an Bijilante da abin ya shafa, Maharazu Abdulmalik, ya ce suna bukatar hukumomi su dauki mataki na doka kan matasan saboda barazanar kashe su a daren karamar Sallah.

‎Biyu daga cikin matasan, Shu’aibu Muhammad da Abdulkadir Abubakar, sun bayyana cewa kwayar da suka sha ne ta sa suka yi tunzura, amma sun nuna nadama tare da alkawarin ba za su sake aikata irin hakan ba.

‎Jaridar Inda Ranka ta ruwaito cewa kakin rundunar Anti-Phone Snaching Force, Ibrahim Garba Ahmad, ya ce tuni kwamandan rundunar, Nura Salisu Sharada, ya bayar da umarnin a mika matasan ga hukumomin da suka dace domin daukar mataki na gaba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending