Connect with us

News

Hatsarin Jirgin Sama Ya Hallaka Matuka Biyu Tare Da Jikkata Sama Da Mutum 40 A Amurka 

Published

on

FB IMG 1774306921187
Advertisements
Advertisements
Spread the love

Akalla matuka jirgi biyu sun rasa rayukansu yayin da sama da mutum 40 suka jikkata sakamakon wani hatsari da ya faru a filin jirgin saman LaGuardia Airport da ke birnin New York.

Hukumomi sun ce hatsarin ya afku ne a daren Lahadi, lokacin da wani jirgi na kamfanin Air Canada ya yi karo da motar kashe gobara a kan titin sauka da tashin jirage.

An Kama Matasa 3  Bisa Zargin Yunkurin Kashe ’Yan Bijilante A Kano  ‎

Advertisement

Bayan hatsarin, an dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a filin na ɗan lokaci, kafin daga bisani a sake bude shi a ranar Litinin.

Rahotanni sun nuna cewa motar ceto na kan aikinta ne bayan an ba ta izinin ketare titin jirgin, amma daga bisani aka umarce ta da ta tsaya cikin gaggawa kafin haduwar ta faru.

Jirgin, ƙirar CRJ-900 da kamfanin Jazz Aviation ke sarrafawa, ya taso ne daga Montreal dauke da fasinjoji 76 ciki har da ma’aikata hudu.

Advertisement

Jami’an tsaro sun tabbatar da mutuwar matukin jirgi da mataimakinsa, yayin da aka kai mutane da dama asibiti.

A halin yanzu, hukumomin Amurka tare da na Kanada sun fara bincike domin gano musabbabin hatsarin, wanda ake ganin shi ne irinsa na farko da ya yi sanadiyyar mutuwar Mutum a filin tun shekarar 1992.

 

Advertisement

PUNCH

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending