Connect with us

News

Jirgin Dakarun Sojin Columbia Ya Yi Hatsari Da Mutane 125 Jim Kadan Bayan Ya Tashi

Published

on

AFP 20260323 A4F99ZQ v2 MidRes TopshotColombiaAccidentDefence 768x513
Advertisements
Advertisements
Spread the love

Akalla mutane takwas ne suka mutu, yayin da wasu da dama suka jikkata, sakamakon hatsarin jirgin dakarun Sojin ƙasar Colombia da ya faɗi jim kaɗan bayan tashinsa daga filin jirgin sama a ranar Litinin.

Jirgin, nau’in Hercules, na ɗauke da sojoji da ma’aikatan jirgi guda 125 lokacin da ya taso daga Puerto Leguízamo, wani yanki da ke kudancin ƙasar kusa da iyakar Ecuador da Peru.

Hatsarin Jirgin Sama Ya Hallaka Matuka Biyu Tare Da Jikkata Sama Da Mutum 40 A Amurka 

Advertisement

Mahukunta sun ce jirgin ya faɗi ne cikin dajin yankin bayan ya kasa samun tsayin da ake bukata bayan tashinsa,

Gwamnan yankin Putumayo, Jhon Gabriel Molina, ya bayyana cewa mutane sama da 80 sun jikkata, yayin da ake ci gaba da aikin ceto a yankinm

Tun da farko wasu majiyoyin soji sun yi hasashen cewa yawan mace-macen na iya karuwa.

Advertisement

Ministan tsaron ƙasar, Pedro Sanchez, ya bayyana hatsarin a matsayin “abin takaici mai matuƙar girma”, yana mai cewa har yanzu ba a tantance musabbabin hatsarin ba.

A nasa bangaren, Shugaban ƙasar Colombia, Gustavo Petro, ya bayyana lamarin a matsayin mummunan haɗari, tare da jaddada buƙatar sabunta kayan aikin sojojin ƙasar.

 

Advertisement

 

 

PUNCH

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending