Connect with us

Politics

Peter Obi, Seyi Makinde sun halarci taron Kwankwaso

Published

on

IMG 20260323 123614 818
Advertisements
Advertisements
Spread the love

Babban ɗan siyasar nan na Nijeriya kuma ɗan takarar shugaban ƙasar na Jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, Rabiu Kwankwaso, ranar Lahadi ya karɓi baƙuncin takwarorinsa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar LP, Peter Obi da Gwamnan Jihar Oyo Seyi Makinde.

Da yake jawabi a wajen gangamin magoya bayan Kwankwaso, Peter Obi ya ce ya kai wa jagoran Kwankwasiyya ziyara ce domin yin gaisuwar Sallah da kuma nuna muhimmancin Kwankwaso a siyasar Nijeriya. Shi ma Seyi Makinde ya jinjina wa Kwankwaso.

HAWAN NASARAWA:Gwamnan Kano Ya Musanta Zargin Yin Watsi Da Sarki Sanusi II

Advertisement

Kwankwaso ya miƙa godiya bisa ziyarar tare da bayyana muhimmancin haɗin kai domin ci gaban Nijeriya.

Masana harkokin siyasa na ganin wannan ziyara na da alaƙa da fafutukar da ‘yan siyasar suke yi wajen ganin sun kawar da Jam’iyyar APC daga mulki a zaɓen 2027 mai zuwa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending