News
Gwamnan Kano Ya Umurci Jami’an Gwamnatinsa Da Ke Son Yin Takara Da Su Yi Murabus
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya umarci dukkan masu riƙe da muƙaman Siyasa da ke da niyyar tsayawa takarar zaɓen 2027 da su yi murabus daga muƙamansu domin bin dokokin da ke ƙunshe a cikin Dokar Zabe.
Umarnin na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da kakakin Gwamnan Sunusi Bature DawakinTofa ya fitar a yau Laraba.
Mun Samu Sunayen Fiye Da Dilolin Kwaya 2,000 A Kano —Rundunar ‘Yan Sanda
Sanarwar ta bayyana cewa saƙon ya zo ya cikin wata takarda da Sakataren Gwamnatin Jiha, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, ya fitar, inda ya jaddada muhimmancin bin dokokin da ke tafiyar da ayyukan jami’an gwamnati.
Takardar ta kuma bayyana cewa wannan mataki ya yi dai-dai da Sashe na 88 (1) na Dokar Zaɓe, wanda ke ƙayyade yadda masu rike da muƙaman gwamnati za su shiga harkokin siyasa.
Takardar ta ƙara da cewa an ɗauki wannan mataki ne domin tabbatar da adalci, gaskiya da riƙon amana a cikin aikin gwamnati, tare da samar da damar daidai ga duk masu neman takara.
Saboda haka, an umurci dukkan masu riƙe da muƙaman siyasa da ke son tsayawa takara da su yi murabus, kafin ranar Talata, 31 ga Maris, 2026
Haka kuma, an umurci dukkan Ma’aikatun Jiha, Sassan Gwamnati da ma’aikatu da su yaɗa wannan sanarwa sosai tare da tabbatar da cikakken bin umarnin.
