Connect with us

News

Dakarun Soji Sun Hallaka ‘Yanta’adda 5 A Filato

Published

on

2026 02 03T182206Z 1 LYNXMPEM12167 RTROPTP 3 USA TRUMP NIGERIA

Dakarun Operation Enduring Peace da ke aikin kawar da ‘yanbindiga a tsakiyar Nijeriya sun kashe mutum biyar da ake zargin ‘yanta’adda ne tare da kama mutum ɗaya da ake zargin mai garkuwa da mutane ne tare da lalata maɓoyar masu aikata laifuka a jihar Filato da ke tsakiyar ƙasar.

A wata sanarwa mai magana da yawun rundunar ta haɗin gwiwa, kyaftin Chinonso Oteh, ya ce dakaru sun yi aikin kakkaɓe masu laifuka sosai ranar Asabar a ƙauyukan Babangida da Adua da Bokayi cikin dajin Dutsen Zaki.

Advertisement

Gwamnatin Tinubu Ta Shirya Kashe Naira Biliyan 135 Domin Shari’un Bayan Zabe

Aikin da aka gudanar tare da ‘yan sa-kai na yankin, ya mayar da hankali ne kan wuraren da masu tayar da ƙayar baya suke a ƙananan hukumomin Wase da Qua’an Pan da kuma Shendam.

Advertisement

“Ƙarfin dakarun da ya rinjayi na masu laifin ya sa an kashe biyu da cikin waɗanda ake zargin nan-take, yayin da wasu suka ja da baya cikin dajin mai duhu da raunuka na harbin bindiga,” a cewarsa.

“Bayan kamen da aka yi daga farko, dakaru sun yi ƙoƙarin lalata maɓoyar waɗanda ake zargin, kuma a lokacin wannan aikin, wasu abokan ‘yanta’addan sun yi harbi kan dakarun.

Advertisement

A cikin hatsaniyar da ta biyo baya, uku daga cikin waɗanda ake zargi huɗu sun yi yunƙurin tserewa amma an harbe su.

“Yayin da suke sintiri a kan hanyar Babangida zuwa Adua, tawagar haɗin gwiwar dakarun ta yi musayar wuta da ‘yanta’adda masu ɗauke da bindigogi,” in ji Oteh.

Advertisement

Ya ce dakaru sun ƙwace makamai da harsasai, ciki har da wata bindiga da aka ƙera a gida da kuma harsasai fiye da 100 masu girman 7.62mm.

An gudanar da wannan aiki ne kwanaki kaɗan bayan tashe-tashen hankula a faɗin jihar Filato, ciki har da kashe-kashe a Angwan Rukuba, ƙaramar hukumar Jos ta Arewa, da kuma hare-haren da suka biyo baya a wasu wurare.

Advertisement

Ƙwanan nan, an kashe mutum uku a wani harin kwanton-ɓauna a ƙaramar hukumar Jos ta Arewa, wani yanayi da ya haddasa ƙarin damuwa daga mazauna jihar da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama kan tashe-tashen hankula da ke daɗa faruwa.

Hukumomin tsaro sun ƙara yawan jami’an da suke turawa da kuma ƙaddamar da ayyukan kakkaɓe maɓoyar masu aikata laifuka a faɗin jihar.

Advertisement

Matakin sojin da aka sabunta ya biyo bayan ziyarar da Shugaba Tinubu ya kai jihar Filato ne a makon jiya, inda ya tabbatar wa mazauna jihar cewa kashe-kashen da aka yi ba za su sake faruwa ba kuma ya bai wa hukumomin tsaro umarnin su zafafa ƙoƙarinsu na dawo da zaman lafiya a jihar.

 

Advertisement

TRT AFRIKA 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending