News
Rashin Rufi da Kujeru Ya Addabi Makarantar Ayaga, Al’umma Sun Nemi Agajin Gwamnatin Kano
Al’ummar garin Ayaga da ke mazabar Rogo Ruma a Ƙaramar Hukumar Rogo, Jihar Kano, sun roƙi gwamnatin jihar da ta gaggauta ceto Makarantar Firamare ta Ayaga, wadda ke fama da matsanancin lalacewar gine-gine da rashin muhimman kayan koyo.
Mazauna yankin sun bayyana damuwarsu ne a wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na ƙaramar hukumar, Malam Abdu Bako Abdullahi (ANIPR), ya fitar, inda suka ce halin da makarantar ke ciki na barazana ga ci gaban ilimin yara a yankin.
Dakarun Soji Sun Hallaka ‘Yanta’adda 5 A Filato
Sarkin yankin, Malam Hamisu Abdullahi, ya ce makarantar ta lalace matuƙa, inda babu rufin ajujuwa, ƙofofi da tagogi, lamarin da ya tilasta wa ɗalibai karatu a ƙarƙashin bishiyoyi.
Ya ƙara da cewa matsalar na ƙara tsananta musamman yayin da damina ke ƙaratowa, wanda ka iya kawo cikas ga karatun ɗalibai.
“Muna kira ga Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya gaggauta ɗaukar mataki domin gyara makarantar, la’akari da muhimmancin ilimi ga cigaban al’umma,” in ji shi.
Wasu mazauna yankin, ciki har da Malam Hamisu Tanga Ayaga da Malam Ibrahim Mai Nama, sun nuna rashin jin daɗinsu kan halin da makarantar ke ciki, inda suka buƙaci gwamnatin jihar ta bai wa shugabannin ƙaramar hukuma damar fara aikin gyara cikin gaggawa.
Haka zalika, shugaban makarantar, Malam Ibrahim Isma’il, ya ce duk da cewa an taba duba halin da makarantar ke ciki a baya, har yanzu ba a ga wani mataki na gyara ba.
Ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta ɗauki matakin gaggawa domin dawo da makarantar cikin yanayi mai kyau da zai dace da koyarwa da koyo.
Al’ummar yankin sun kuma yabawa shugabannin ƙaramar hukumar bisa ƙoƙarinsu, tare da roƙon su da su isar da ƙorafin zuwa ga gwamnatin jihar domin a samu mafita cikin gaggawa.
