Connect with us

News

Amurka Da Iran Sun Amince Da Tsagaita Wutar Kwanaki 14

Published

on

5a2a6960 9bc7 4226 954b 1897b5d19e7b.jpg

Bayan kai ruwa rana na tsawon makwanni Iran ta amince da tsagaita wutar kwanaki 14 a yaƙin da ta ke gwabzawa da Amurka wanda aka faro tun a ranar 28 ga watan Fabarairu, yaƙin da bai yiwa dukkanin ɓangarorin da ke cikinsa daɗi ba.

Pakistan wadda ke matsayin babbar mai shiga tsakani a wannan yaƙi da taimakon ƙasashen Masar da kuma Turkiyya ne suka jagoranci miƙa daftarin yarjejeniyar tsagaita wutar a lokuta daban-daban ga Iran, sai dai sai a jiya ne Tehran ta amince amma fa na kwanaki 14 saɓanin 45 da Amurkan ta buƙata, yayinda za a faro tattaunawa ranar Juma’a kan buƙatun da kowanne ɓangare da shi tare da daidaitawa akan turbar da za a fahimci juna.

Advertisement

‎Kotu Ta Tsare Matar Aure Bisa Zargin Kashe Jaririn Mijinta A Kano

Tun a daren jiya kafin kowanne ɓangare ya sanar da wannan jituwa, aka ga yadda Donald Trump ya sanar da cewa ya tsagaita kai hare-haren bayan da a cewarsa Pakistan ta nemi ya jinkirta gabanin sanarwar Iran da ke cewa ta aminta da tayin tsagaita wutar, sa’o’i ƙalilan gabanin wa’adin Trump da ke cewa zai yiwa ƙasar luguden wutar da bata taɓa gani ba.

Advertisement

Sharaɗi na farko kamar yadda shi Donald Trump na Amurka ya faɗa shi ne ganin Iran ta buɗe mashigin Hormuz wanda ta kulle tun kwanaki ƙalilan bayan faro wannan yaƙi, sai dai fa an jiyo ministan wajen Iran Abbas Aragchi na cewa jirage zasu samu sukunin ratsa mashigin na Hormuz wajen gudanar da hada-hadarsu ta tsawon makwanni 2 ne kaɗai yayinda ƙasar za ta sake kulle shi, wanda ya sanya fargabar cewa da yiwuwa yaƙin bai ƙare ba.

Kamar yadda aka yi tsammani dai ƙasashe da dama sun yi maraba da wannan yarjejeniyar ciki har da Majalisar ɗinkin duniya da ita kanta Isra’ila da ake ganin tun farko ita ce Amurka ta ke yiwa wannan yaƙi, inda aka jiyo ƙasar ta Yahudu na maraba da matakin kodayake ta ce tsagaita wutar bai shafi luguden wutarta a Lebanon ba.

Advertisement

Sai dai fa har zuwa yanzu ba a jiyo ɗuriyar manyan ƙasashen yammaci wajen maraba da wannan yarjejeniya ba, haka zalika babu manyan ƙasashen Larabawa.

Tun farko kaso mai yawa na Amurkawa basa tare da Trump a wannan yaƙi wannan nema ya sanya mishi fuskantar kakkausar suka musamman daga ɓangaren Democrats, inda aka jiyo wani babban mashawarcin tsohon shugaba Barrack Obama Ben Rhodes, a tsokacinsa kan tsagaita wutar na cewa yaƙin na Trump a Iran shi ne mafi munin lamari ga Amurka.

Advertisement

A gefe guda ita kanta Republican ta matsa lamba ga Trump kan ya dakatar da yaƙin saboda barazanar da jam’iyyar ke fuskanta a zaman tsakiyar wa’adi sakamakon yadda yaƙin ya haddasa matsin rayuwa ga ƴan ƙasar.

A ɓangaren Iran kuwa, mahukuntan ƙasar aka jiyo suna jinjina ga ɗaukacin jama’ar ƙasar waɗanda suka bayyana da jajirtattu masu cike da ƙwarin gwiwa.

Advertisement

A tsakar biranen Iran da wannan safiya dai wani biki ake gudanarwa na musamman na ƙone tutocin ƙasashen Isra’ila da Amurka inda aka ga dandazon jama’a suna wannan aiki na gamawayya.

 

Advertisement

 

RFI

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending