Bisa sabon tsarin, dokar hana fitar za ta kasance daga ƙarfe 6:00 na yamma zuwa 6:00 na safiya a kowace, daga ranar Laraba, 8 ga Afrilun 2026, kamar yadda wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Kwamishinar Yaɗa Labarai da Sadarwa, Joyce Lohya Ramnap, ta tabbatar.
Trump Ya Amince Da Tsagaita Wuta Tsawon Mako Biyu Idan Iran Ta Bude Mashigar Hormuz
Gwamnatin ta kuma umarci hukumomin tsaro da su tabbatar da cikakken bin dokar hana fitar domin kare rayuka da dukiyoyi tare da tabbatar da ɗorewar zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa.
Duk da ingantuwar yanayin tsaro, hukumomi sun buƙaci mazauna Jos da su ci gaba da kasancewa masu bin dokar yadda ya kamata, tare da bai wa jami’an tsaro haɗin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai da za su taimaka wajen magance duk wata barazana ga zaman lafiya.
Gwamnatin ta kuma sake jaddada aniyarta na dawo da cikakken zaman lafiya da daidaito a faɗin Jos Arewa da sauran sassan jihar.
