Connect with us

News

‎Kotu Ta Tsare Matar Aure Bisa Zargin Kashe Jaririn Mijinta A Kano

Published

on

‎Wata kotun majistare da ke zamanta a Kano ta umarci a tsare wata matar aure, Zayya Magaji, bisa zargin kashe ƙaramin ɗan mijinta ta hanyar ba shi guba.

‎Ana zargin matar, mazauniyar ƙauyen Danbango a ƙaramar hukumar Kabo ta Jihar Kano, da haddasa mutuwar yaron mijinta mai shekara uku.

Advertisement

Gwamnatin Filato Ta Sassauta Dokar Hana Fita A Jos

‎Lauyan gwamnati, Barrista Muhammad Aliyu, ne ya gurfanar da ita a gaban kotu, inda magatakardar kotu, Nafiu Sani, ya karanta mata tuhume-tuhumen da ake yi mata.

Advertisement

‎A cewar masu gabatar da ƙara, matar ta aikata laifin ne ta hanyar ba yaron guba, wanda hakan ya janyo mutuwarsa.

‎Sai dai wadda ake tuhuma ta musanta zargin, tana mai cewa ba ta aikata laifin da ake zarginta da shi ba.

Advertisement

‎Lauyan gwamnati ya kuma bayyana wa kotu cewa an tura takardun shari’ar zuwa Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano domin samun shawarar doka kafin ci gaba da shari’ar.

‎Alƙalin kotun, Mai Shari’a Auwal Yusuf, ya amince da buƙatar dage shari’ar, tare da bayar da umarnin a tsare wadda ake zargin a gidan yari.

Advertisement

‎Kotun ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 29 ga watan Afrilu, domin ci gaba da shari’ar.

 

Advertisement

 

DAILY TRUST 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending