News
Trump Ya Amince Da Tsagaita Wuta Tsawon Mako Biyu Idan Iran Ta Bude Mashigar Hormuz
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana aniyarsa ta amincewa da tsagaita wuta na tsawon mako biyu tsakanin Amurka da Iran, muddin Tehran ta amince ta buɗe mashigar ruwan Strait of Hormuz.
Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ake jiran cikar wa’adin da Trump ya bai wa Iran domin sassauta matsin lamba da ke tattare da rikicin diflomasiyya tsakanin kasashen biyu.
Rashin Rufi da Kujeru Ya Addabi Makarantar Ayaga, Al’umma Sun Nemi Agajin Gwamnatin Kano
A cewar rahotanni, shirin tsagaita wutar na da nufin rage zafin rikicin da ya dade yana ƙara kamari, tare da bai wa bangarorin damar komawa teburin sulhu.
Haka kuma, an rawaito cewa kasar Pakistan ce ta jagoranci shirya wata muhimmiyar ganawar diflomasiyya tsakanin Amurka da Iran, wadda aka gudanar a ranar Talata, domin samar da mafita mai dorewa ga takaddamar.
Mashigar Hormuz na daya daga cikin muhimman hanyoyin zirga-zirgar man fetur a duniya, kuma duk wani cikas a cikinta na iya janyo tasiri mai girma ga tattalin arzikin duniya baki daya.
