Connect with us

News

Gobara ta ƙone shaguna a kasuwar Hajj Camp da ke Kano

Published

on

Spread the love

Daga kabiru basiru fulatan

 

 

Gobara ta ƙone shaguna huɗu a kasuwar sansanin alhazai ta Kano wato Hajj Camp.

Advertisement

Gobarar ta tashi ne a daren Jumu’a lokacin buɗa baki, a ɓangaren masu sayar da kayan Gumama.

Shugaban kasuwar Alhaji Auwal Ahmad Shinkafi ya tabbatarwa da Freedom Radio faruwar lamarin.

Ya ce “Wutar ta tashi bayan an sha ruwa, ta ƙone shaguna huɗu, an yi asarar dukiya ta miliyoyi”.

“Zuwa gobe idan Allah ya kaimu zamu tantance adadin asarar da aka yi, mun kira ƴan kwana-kwana da jami’an tsaro, kuma duka sun bamu gudunmuwa har aka kashe gobarar”.

Advertisement

Alhaji Shinkafi ya jajantawa ƴan kasuwar da lamarin ya shafa.

Ana fargabar rasa rayuka tare da jikkatar sama da mutane 50 sanadiyyar gobara a Kano

Hajiya Aisha Abduljalal na cikin waɗanda shagunansu ya ƙone ƙurmus ta shaida wa Freedom Radio yadda labarin ya risketa.

“Ina gida ina shan ruwa aka min waya cewa shagona ya kama da wuta, na hawo babur na zo, sai na tarar babu abin da zan ɗauka, jiya na zaba kaya, yau ma na ƙara zubawa saboda fatan cinikin sallah, sai ga wannan tsautsayi” a cewarta.

Advertisement

Ta ƙara da cewa “A hakanmu babu abin da zance sai godiyar ubangiji, aƙalla kayan da suke cikin shagona sun kai miliyan uku amma ban ɗauki komai ba”. Hajiya Aisha ta ƙarasa maganar cikin shashsheƙar kuka saboda alhini.

Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta Kano SFS Saminu Yusuf Abdullahi ya tabbatarwa da Freedom Radio faruwar lamarin, har ma yace tuni jami’ansu suka kai ɗauki.

 

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *